USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram
Published: 19th, February 2025 GMT
Gwamnatin Amurka ta ƙudiri aniyar gudanar da bincike kan yadda gwamnatocin da suka gabata suka riƙa sarrafa kuɗaɗen da aka fitar domin bai wa Nijeriya da wasu ƙasashen tallafi.
Hakan dai ya biyo bayan matakin da Shugaban Amurkan, Donald Trump ya ɗauka a watan Janairu na dakatar da duk wani tallafi da Amurkan ke bayarwa a ƙetare har na tsawon kwanaki 90.
Shugaba Trump ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta gudanar da binciken ne a dalilin ruɗanin da ya dabaibaye duniya wanda ke cin karo da muradun Amurkan.
Haka kuma, Shugaba Trump ya ce za a gudanar da binciken ne domin amsa kiraye-kirayen ke yi wajen bitar ayyukan da Hukumar Bayar da Agaji ta USAID.
A bayan nan ne wani ɗan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya bayyana cewa hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID) ke samar da kuɗaɗe ga kungiyoyin ’yan ta’adda, ciki har da Boko Haram.
Perry ya yi wannan iƙirarin ne yayin zaman sauraron rahoton kwamitin majalisar a kan yadda hukumomin gwamnatin Amurka ke aiwatar da ayyuka da sarrafa kuɗaɗe a ranar Alhamis ta makon jiya.
Zaman mai taken “yaki da barna: Kawar Da Annobar Almundahana Da Zamba,” ya maida hankali ne a kan zargin barnatar da kudaden masu biyan haraji.
“Waye ke samun wani banagare na kudaden? ko wani a ɗakin nan ya kiyaye waɗannan sunaye? saboda kudadenku, dala miliyan 697 a duk shekara, baya ga aika ƙarin kuɗaɗe ga Madrasas da ISIS da Al-Qa’ida da Boko Haram da ISIS Khorasan da sansanonin horas da ‘yan ta’adda. Wadannan su ne abubuwan da take daukar nauyi,” kamar yadda Perry ya bayyana.
Shafin yanar gizon kwamitin ya bayyana cewar zai yi aiki tare da ma’aikatar bin diddigin ayyukan hukumomin gwamnatin Shugaba Trump domin magance barna, da dakile almundahana tare da gudanar da cikakken bincike a kan yadda aka zambaci masu biyan harajin Amurka.
Ƙungiyar Boko Haram, wacce aka sani da Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, ƙungiya ce ta ‘yan ta’adda da ta ayyana kanta a matsayin mai tayar da ƙayar baya yankin arewa maso gabashin Nijeriya, da kuma ƙasashen Chadi, Nijar, Kamaru da kuma Mali.
Ƙungiyar ta shafe sama da shekaru 15 tana tashe-tashen hankula a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya, inda ta kashe dubun-dubatar mutane, a hare-haren da take kai wa ’yan sanda, da sojoji da fararen hula.
Zan gabatar da ƙudiri… — NdumeA kwanan ne shi ma Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ya buƙaci gwamnatin Nijeriya ta gaggauta gudanar da bincike kan iƙirarin da ɗan majalisar dokokin Amurka ya yi na cewa hukumar USAID da gwamnatin Trump ta rufe ta tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci da suka haɗa har da Boko Haram a ƙasar.
Ndume ya ce ba batu ba ne da ya kamata gwamnatin Nijeriya ta naɗe hannunta, la’akari da girman barnar Boko Haram a Jihar Borno.
Ya ce zai gabatar da ƙudiri kan binciken zargin ɗan majalisar dokokin na Amurka.
“In an tashi binciken za mu yi tambayoyi, saboda haka za mu bincika domin mu ’yan Nijeriya da abun ya shafa ya kamata mu sa ido don a san matakan da za a ɗauka, saboda ba ƙaramin ɓarna Boko Haram suka yi mana ba,” in ji Ndume.
BBC ya ruwaito Sanata Ndume yana zargin cewa USAID ba ta aiki tare da hukumomin da ya kamata ta yi aiki tare da su a Nijeriya, lamarin da ya ke dasa ayar tambaya.
“Ba sa bari jami’an tsaronmu su sanya ido kan abubuwan da suke yi ballantana su ba da shawara.”
An dai ƙirƙiri Hukumar USAID a shekarun 1960 domin taimaka wa ayyukan agaji a madadin gwamnatin Amurka a kowanne yanki na duniya.
Tana da ma’aikata dubu 10, wanda kashi biyu bisa uku na aiki a ƙetare. Tana da cibiyoyi a sama da ƙasashe 60, sannan tana ayyuka daban-daban a sauran ƙasashe.
Sai dai galibin ayyukanta wasu ƙungiyoyin take bai wa kuɗi su aiwatar, nata shi ne sa ido da tabbatar da cewa an kashe kuɗaɗen bisa tsari.
Ayyukanta na da dimbin yawa. Misali, USAID ba tallafin abinci kaɗai take bayarwa a ƙasashe masu fama da yunwa ba, tana kuma aiki wajen gane inda za a fuskanci fari, da kuma inda za a buƙaci agajin gaggawa na yiwuwar ƙarancin abinci a nan gaba.
Galibin kasafin kuɗin USAID ana kashe su ne a fannin lafiya, irin su rigakafin Polio a ƙasashen da cutar ke yaɗuwa da kuma taimakawa wajen daƙile yaduwar cututtuka da ake yi wa kallon annoba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram gudanar da bincike a gudanar da
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da shirin noman rani na Lallashi
A kokarin Gwamnatin Jihar Jigawa na karfafa ayyukan noman rani tare da samar da wadataccen abinci da inganta rayuwa, ta kaddamar da shirin noman rani na Lallashi da ake amfani da rijiyoyin burtsatse a Karamar Hukumar Maigatari ta jihar.
Rahoton na nuna cewa, an yi aikin ne domin canza salon noman rani da sauran ayyukan noma a yankunan da galibi hamada ce.
A cewar rahoton, wannan shiri ana yin amfani da makamashin hasken rana da kuma amfani da na’urori masu rahusa tare da dabarun noman rani don samar da harkokin noman rani mai inganci cikin sauki.
Dakatar da Gwamnan Ribas zubar da ƙimar Nijeriya ne a idon duniya — Jonathan An ayyana zaman makoki na kwana uku bayan kashe mutum 44 a NijarDa yake jawabi a lokacin kaddamar da aikin, Gwamna Umar Namadi ya bayyana muhimmancin aikin, inda ya bayyana hakan a matsayin wata hanya ta jaddada kudirin gwamnatinsa na ganin an samar da abinci mai yalwa da samar da hanyoyin rayuwa mai dorewa da rage radadin talauci a tsakanin al’umma.
Ya kuma bayyana cewa, babban abin da gwamnatinsa ta sanya a gaba shi ne na cimma manufofin kudirorinta 12 wajen amfani da hanyoyin noma na zamani a Jihar Jigawa, musamman ta hanyar gudanar da ayyukan noma a duk shekara.
Ya kara da cewa, gwamnatinsa na daukar matakai daban-daban don gyara da fadada wuraren noman rani a fadin jihar da suka hada da samar da madatsun ruwa da rijiyoyin burtsatse na yau da kullum.
Sai dai an bayyana cewa shirin noman na Lallashi da rijiyar burtdatse ya kunshi gonaki hekta 10 kuma yana samun tallafin manyan rijiyoyin burtsatse irin na masana’antu guda hudu, kuma ya zuwa yanzu, manoma sama da 80 ne ke cin gajiyar shirin kai-tsaye, wanda ake sa ran zai bunkasa noman sosai da kuma yaukaka tattalin arziki.
Da yake jawabi a madadin manoman yankin, malam Aliyu Musa ya bayyana cewa, abin da gwamnati ke yi wa al’ummomin da ke kewayen wurin noman rijiyoyin burtsatse tamkar jari ta bayar na rayuwa da ba za a iya tantance adadinsa ba.
A cewarsa, jama’a za su ci gaba da addu’o’in samun nasarar shirin tare da fadada shirin domin kara fadada shi a yankunan jihar gaba daya.
“Da farko mutanen wannan yanki suna yin noman rani ne da zarar lokacin damina ya kare, amma labarin ya canza a yanzu, wanda ke nufin ba za a bar kauye zuwa birni ba don ci-rani.
“Nan ba da dadewa ba birni zai zo gare mu, yayin da muka fara nazarin wannan dama mai albarka ta tashi a matsayin al’ummomin da ke da wuraren noman rani,” inji shi.