Kissoshin Rayuwa. Sirar Imam Alhassan (a) 19
Published: 19th, February 2025 GMT
19-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa Shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na shahid Aya. Murtadha muttahhari, ko cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddeen, Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.
///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan (s) Jikan manzon All..(s) sannan limami na 2 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) kuma da, na farko ga Fitima(s) diyar manzon All..(s).
A cikin shirimmu da ya gabata, mun kawo maku yadda aka zabi Khilifa na farko da kuma yadda wasu daga cikin sahabban manzon All..(s) suka ki amincewa da bai’at tasa.
Na gaba-gaba daga cikin wadanda suka ki yi masa bai’a shi ne Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a), sannan akwai Sa’adu dan Ubada, shugaban kabilar Hazraju daga cikin Ansar, sannan minji makomar sa a lokacinda aka tsinci gawarsa a cikin wata rijiya a hanyar sha.
Sannan mu fara kawo mauki dalilai da hujjoji wadanda Imam Ali (a) da kansa ya gabatarwa Khalifa na farko dangane da cancantarsa, da hakkinsa na kujerar Khalifanci bayan wafatin manzon All..(s).
Imam Ali (a) bayan an yiwa Abubakar dan Abu Kuhafa, bai’a a matsayin Khalifan manzon All..(s), ya nuna bacin ranasa ya kuma bayyana rashin amincewarsa, ya na ganin hakkinsa ne ya kwace, kuma ya bukaci a mayar masa da hakkinsa.
Malaman tarihi sun bayyana cewa Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a) ya kafa hujjoji da dama don dawo da hakkinsa daga hannun Abubakar. Wannan ya faru ba sau guda ba, inda a cikinsu gaba daya, ya bayyana masu shi ne mai hakki, saboda matsayinsa a cikin musulmi, shi ne na farkon musulunta, ya fi dukkan sahabbai ilmi, ya kasance jarumi a mafi yawan yake-yaken musulunci.
*-Da farko, a lokacinda aka kama shi daga cikin gidansa, a dabaibaye cikin igiyoyi aka kawo shi masallaci a gaban Abubakar, sai aka ce masa kayi wa Abubakar bai’a, sai ya basu amsa, al-hali yana dabaibaye cikin igiyoyi. (Ni nafi cancanta da ku yi mani bai’a, b azan yi maku bai’a ba. Na fi cancanta ku yi mani bai’a. Kun karbi wannan al-amarin daga Ansaru, kun hujjacesu da kusanci da manzon All..(s). Sannan kun karbeshi daga iyalan gidan manzon All..(s) da karfi. Shin baku fadawa Ansar kan cewa ku ne makusantar manzon All…S ba, kun ce ku kuka fi cancanta da wannan al-amari, tunda manzon All..yana fito ne daga cikinku ba, sai suka mika maku wuya. Suka sallama maku shugabanci?. Don haka nima ina hujjace ku da abinda kuka hujjace Ansar da shi, kan cewa mu muka fi cancanta da al-amarin manzon All..(s) a raye da kuma bayan mutuwarsa….) don haka amirulmuminina ya shiga ta hanyar da Muhajirun suka bi wajen kwace hakkinsa, y ace masu, abinda kuaka fada faskiya ne, ammma ni kuma ina kafa maku hujja kan cewa mu munfi kusa da manzon All..(s) kanku, ku mika mana shugabancimmu mu.
Idan a dangantaka ne, shi dan’ammin manzon All.. kuma surukinsa ne da hanyar diyarsa Zahra’ (s).
A lokacinda dankhaddani ya ji wannan hujjar sai ya fito ta wata hanyar, ta nuna karfi, inda yace baza’a barkaba sai kayi bai’a
Sai Imam Ali ya daga murya, yana cewa masa: (Ka tasha masa, ka na da rabinsa. Ka rike masa al-amari a yau sai ya mayar maka da shi gobe.}
Sai Imam (a) ya kara da cewa: Na rantse da All..Ya Umar b azan karbi zancenka ba, kuma ba zanyi bai’a ba.).
Sai Abubakar ya ji tsoro kan abinda karshensa ba zai yi dadi ba, sai ya zo kusa da Aliyu (a) yana cewa: Idan kaki kayi bai’a ba zama tilasta maka ba.
A wani bangare kuma Ubu ubaida dan Jarra, yayi kokarin gamsar da Imam yayi bai’a a hankali, sai y ace masa: Ya dana mmi na, kai shekarunka kadanne, wadannan dattawan mutanenka ne, baka da korewa da kuma sanin al-amura kamarsu ba. Ni bana ganin face, Abubakar ya fika sanin al-amura fiye da kai. Ya fika sani da kuma gogewa a kansa. Ka sallamawa Abubakar wannan al-amari, don lalle idan ka yi tsawon rai, kai ka cancanci wannan matsayin, saboda falalarka, da adininka da kuma ilminka. Sannan ga kusancinka, da suurukantakarka, da kuma da saurin fahintarka da kuma kekyawar matsayinta a tarinin addinin musulunci. ..}
Magabar Abu Ubaida dan jarrah, ya ingiza Imam (a) yana magana wa, dukkan muhajirun ya na fadar abubuwanda All…ya fifita iyalan gidan manzon All..(s) da su. (Ina hadaku da All..ina hadaku da All..ya ku masu hijira, kada ku fitar da shugabancin Muhammadu a cikin larabawa daga gidan shi. Daga tsakiyar gidansa, ku maida shi gidajenku, a kuma tsakiyar gidajenku. Kada ku tumbuke iyalan gidansa daga matsayinsa a cikin mutane da kuma hakkinsa.
Na ranste da All..ya ku muhajirun wallahi mu muka fi cancanta da wannan al-amarin da ku, – don mu iyalan gidansa-saboda wadanda suka kasance masu karatun al-kur’ani cikimmu, da ilimin sanin addini, da kuma masana sunnar manzon All..(s), da kuma sanin al-amuran Jagoranci, da kuma mai tunkude wa al-umma mummunan abinda ke tunkararsu, kuma wanda zai yi rabo a tsakaninsu dai-dai,(babu nuna fifiko). Wallahi lalle – mai wadannan sifofi yana cikimmu- kada ku bi son zuciya ku bace daga tafarkin All..sai ku kara nisanta daga All…),
Da wannan khudunar Imam (s) ya tunkudewa mutanen duk wata shubha, bai bar masu wata kofa face ya rufe ta, da wannan khuduba mai fasaha da kuma bayyana gaskiya.
Wannan kuma ya ture duk abinda Ubu ubaida dan jarra ya yi riko da shi don kare Abubakar a kan abinda yake kai, na cewa shi ne yafi amirul muminina (a) shekaru.
Imam (s) ya nuna masu cewa, wanda ya mallaki abubuwan da ya ambata din nan sune wadanda ake mizanin shugabanci da su a musulunci. Kuma su ya cancanci zama mai kula da al-amuran musulmi.
Sannan addinin All.., da sanin sunar manzon All..(s) da sanin makamar aiki na kula da al-amuran mutane, da tunkede masu mummuna, da rabo tsakaninsu da adalci, wadannan sune sifofinda musulunci yake kula da su, a matsayin abin lura wajen kuma ba wanda yake da wadannan sifofi sai a cikin iyalan gidan manzon All…(s). wannane ya sa suka kasance, wadanda suka fi cancanta da wannan al-amari fiye da kowa.
Har’ila yau Zahra’u (s) shugaban matan Aljanna ta hujjacesu da wasu hujjojin kwarara, kan mumunan abinda ta aikata, da babban laifin da suka aikata. Tana fada (s) a cikin wata khudubarta kan cewa:
Kaitonku, ina suka kaita-wato khalifancin-daga barin – makafar annabci, da ginshikan annabcic, masaukar ruhun Ameen. Masanan ilmin adini da duniya, Ku saurar ! wannan shi ne asara babba. Kuma menene suke ganin tawaya ne a wajen baban Hassan? Suna sukansa- wallahi-kaifin takobinsa da kuma tsananin damkarsa.
A cikin khudubar (s) ta gutsurowa musulmi ilmin gaibun da All..ko manzonsa suka sanar da ita. Ta cewa masu zuwa a bayan zasu dandani mummunan aikin da magabata suke. Don haka an haramtawa na baya saboda kurakuran da magabata suka yi.
Da musulmi muminai a cikin sahabban manzon All…(s) sun amince da Amirul muminina (a) a matsayin shugaba a lokacin, da sun ci ta sama da kasa, da kuma karkashin kafafuwansu. Da kuwa basu jawowa al-ummun baya sharrin da musibun da suka fadawa musulmi tun lokacin hzr zuwa yanzu ba.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: iyalan gidan manzon All wannan al amari masu sauraro wadanda suka
এছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karɓar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade.
Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma?
NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar HausaShirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita.
Domin sauke shirin, latsa nan