Rasha Ta Kakkabo Jiragen Sama Marasa Matuki 9 Na Kasar Ukiraniya
Published: 19th, February 2025 GMT
Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da cewa, ta kakkabo jiragen saman marasa matuki 9 da kasar Ukiraniya ta harba mata.
Sanawar ta ma’aikatar harkokin tsaron Rasha ta ci gaba da cewa; A daren jiya ne aka kakkabo jiragen sama marasa matuki 3 na kasar Ukiraniya da aka harba a kan yankin Biryansk, sai kuma wani jirgin saman guda daya akan sararin samaniyar Tatrastan.
A gefe daya a jiya ne aka bude wani kwarya-kwaryar taro a tsakanin kasashen Amurka da Rasha a kasar Saudiyya domin tattauna hanyoyin kawo karshen yakin Ukinraniya.
Sakataren harkokin waje na kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa kasashen Amurka da Rasha sun kuduri anniyar kawo karshen yakin Ukrai.
A taron na jiya dai babu wakilin kasar Ukraine, wacce da alamun ta kasa samun nasara a yakin da ta shiga da Rasha kimani shekaru 3 da suka gabata.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Firaministan Kasar Laos: Kasar Sin Abar Koyi Ce a Fannin Kawar Da Talauci
Sa’an nan, dangane da layin dogon da wani kamfanin kasar Sin ya gina, wanda ya hada kasar Laos da kasar ta Sin, mista Siphandone ya ce, layin dogon ya haifar da alfanu sosai, a fannin tattalin arziki, wanda ya zarce yadda aka zata a baya. Kana wannan layin dogon zai zama wani bangaren sabon layin dogon da ya hada kasar Sin da kasar Singapore, wanda za a shimfida shi a nan gaba. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp