Sojojin Sudan Sun Killace Fadar Shugaban Kasa Da Take A Hannun ‘Yan Tawayen A Birnin Khartum
Published: 19th, February 2025 GMT
Rundunar sojan kasar Sudan ta sanar da kwace iko da hanyoyin da suke isa al-Fasha, kamar kuma yadda su ka killace fadar shugaban kasa dake birnin Khartum.
Sanarwar sojojin na Sudan ta kuma tabbatar da cewa, killace wannan hanyar da su ka yi, ya yanke duk wata dama da dakarun “Rundunar Kai Daukin Gaggawa” suke da ita, ta samu dauki.
Birnin al-Fasha dai shi ne babbar birnin jahar Arewacin Darfur, kuma sojojin na Sudan sun ce, suna ci gaba da kutsawa a cikin jahar.
A gefe daya, wani jami’in sojan Sudan Yasir Adha, ya sanar da cewa; Babu yadda yaki zai tsaya har sai an ‘yanto da kowane taku daya na kasar Sudan daga hannun ‘yan tawaye.
Adha ya bayyana hakan ne dai a gaban sojoji a birnin Dabbah dake jahar Arewacin kasar.
A nashi gefen gwamnan jahar Darfur, Muna Minawi ya ce, sojojin na kasar Sudan suna ci gaba da ‘yanto da garuruwan kasar har zuwa birnin Janinah da shi ne babban birnin jahar Darfur ta yamma.
Haka nan kuma ya yi kira ga dukkanin masu goyon bayan “Rundunar Kai Daukin Gaggawa” a wannan yankin da su daina.
A cikin birnin Khartum kuwa sojojin Sudan sun katse duk wata hanyar kai musu dauki zuwa kusa da fadar shugaban kasa. A halin yanzu dai an killace “Dakarun Kai Daukin Gaggawa” dake cikin kusa da fadar ta shugaban kasa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Ya Mika Ta’aziyyar Ta Rasuwar Wanda Ya Assasa Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Iran
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana alhininsa akan rasuwar Dr. Akbar I’itimadi wanda shi ne na farko da ya kafa hukumar makamashin Nukiliya ta Iran.
Wasikar ta’aziyyar da shugaban kasa ta kunsa ta ambaci cewa: Shakka babu hidima mai kima da wannan masanin ya yi, ya share fagen gina da ci gaban fasahar makamashin Nukiliya a Iran da kuma mayar da kasar mai cin gashin kanta a wannan fage.
Har ila yau, shugaban kasar ta Iran ya mika sakon ta’aziyyarsa ga masana na Iran, da kuma iyalansa. Ya kuma yi addu’a da rokon Allah madaukin sarki da ya lullube shi da rahamarsa da kuma gafararsa, sannan ya bai wa iyalansa na hakuri.