Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan Tsaro
Published: 19th, February 2025 GMT
Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya gargaɗi ƙasashe cewa Najeriya ba za ta yarda da rashin girmamawa daga kowace ƙasa ba.
Ya bayyana hakan ne bayan da Ƙasar Kanada ta hana wasu jami’an sojin Najeriya takardae izinin shiga ƙasar, duk da cewa an gayyace su don halartar wasannin Invictus a Vancouver.
Da yake jawabi a Hedikwatar Tsaro da ke Abuja, bayan tarbar sojojin da suka halarci gasar, Musa ya nuna takaicinsa kan yadda ake nuna wa ‘yan Najeriya rashin adalci a wasu ƙasashe.
“Mun bi dukkanin matakan da suka dace. An aiko mana da gayyata, jami’an gwamnati sun sani, kuma mun cika dukkanin sharuɗa.
“Amma, ba san dalilin da ya sa aka hana jagororin tawagarmu kamar kaftin, likitan tawaga da mai duba biza. A. Tambayar ita ce, me ya sa?” in ji shi.
Musa ya jinjina wa sojojin da suka wakilci Najeriya a gasar, inda ya tabbatar musu da cewa gwamnati ba za ta bari su wulaƙanta ba.
“Sojojinmu da suka rasa wasu sassa jikinsu ko suka samu raunuka ba za a bari a wulakanta su ba.
“Za mu ci gaba da tallafa musu domin sadaukarwarsu ba za ta tafi a banza ba,” in ji shi.
Ya jaddada cewa Najeriya ta cancanci girmamawa, kuma ba za ta yarda da rashin adalci daga kowace ƙasa ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babban Hafsan Tsaro Janar Musa
এছাড়াও পড়ুন:
Wike Ya Kwace Filaye 4,794 A Abuja Saboda Rashin Biyan Kudin Ka’ida
“Saboda haka, za a soke sunayen kadarorin da suka shafe sama da shekara goma ba a biya musu haraji ba nan take, Bugu da kari kuma, ana bayar da wa’adin kwanaki 21 ga masu rike da gidajen da ake rike da bashin kudin haraji na tsawon shekara daya zuwa goma, sannan kuma za a soke sunayensu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp