Kasar Iran Ta Jaddada Aniyarta Ta Daukan Fansa Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Published: 19th, February 2025 GMT
Kwamandan dakarun juyin juya halin Musulunci na rundunar sararin samaniya ya jaddada cewa; Babu shakka Iran zata kaddamar da harin daukan fansa kan haramtacciyar kasar Isra’ila na alkawarin gaskiya na 3
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na rundunar Sojin sararin samaniyar Iran, Birgediya Janar Amir Ali Hajizadeh, ya jaddada cewa za a gudanar da farmakin daukan fansa na Alkawarin Gaskiya na 3 idan Allah Ya yarda, amma Iran ba zata barnatar da kwarewarta a banza kamar yadda ya faru a harin alkawarin Gaskiya ta 1 da ta 2 ba, don haka babu shakka za a gudanar da harin daukan fansa kan haramtacciyar kasar Isra’ila.
Ya kara da cewa: Yankin yammacin Asiya ya samu ci gaba da dama, kuma wannan yanki shi ne tushen al’amuran duniya da dama, to amma a baya-bayan nan ya fara ne da harin daukan fansa na Ambaliyar Al-Aqsah wanda kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta tsara ta kuma aiwatar da shi, wanda ya zama babbar nasara a kan ‘yan sahayoniya, wannan lamari ne mai muhimmanci.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Ya Mika Ta’aziyyar Ta Rasuwar Wanda Ya Assasa Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Iran
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana alhininsa akan rasuwar Dr. Akbar I’itimadi wanda shi ne na farko da ya kafa hukumar makamashin Nukiliya ta Iran.
Wasikar ta’aziyyar da shugaban kasa ta kunsa ta ambaci cewa: Shakka babu hidima mai kima da wannan masanin ya yi, ya share fagen gina da ci gaban fasahar makamashin Nukiliya a Iran da kuma mayar da kasar mai cin gashin kanta a wannan fage.
Har ila yau, shugaban kasar ta Iran ya mika sakon ta’aziyyarsa ga masana na Iran, da kuma iyalansa. Ya kuma yi addu’a da rokon Allah madaukin sarki da ya lullube shi da rahamarsa da kuma gafararsa, sannan ya bai wa iyalansa na hakuri.