Shugaban Kasar Iran Ya Tattauna Da Sarkin Kasar Qatar Kan Muhimmancin Hadin Gwiwa Da Taimakekkeniya Tsakaninsu
Published: 19th, February 2025 GMT
Shugaban kasar Iran da Sarkin kasar Qatar sun jaddada muhimmancin hadin gwiwa da taimakekkeniya tsakanin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamid Al Thani sun gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Tehran, inda suka jaddada karfin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma muhimmancin kara inganta taimakekkeniya a tsakanin kasashensu.
Shugaban na Iran ya fada a yammacin yau Laraba cewa: Ci gaba da tarukan tsakanin jami’an kasashen biyu ke yi na tabbatar da kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu, yana mai jaddada karfafa alaka da kasashe makwabta, musamman kasar Qatar, a matsayin wani muhimmin ka’ida na manufofin ketare na Iran.
Shugaban kasar ya ci gaba da cewa: Sun tattauna da Sarkin Qatar kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu ta hanyar da za ta tabbatar da moriyar kasashensu, kuma an yanke wasu muhimman shawarwari na raya kasa da zurfafa dangantaka da bude sabbin hanyoyin hadin gwiwa. Sarkin Qatar ya kuma jaddada bukatar samar da sabbin damar gudanar da hadin gwiwa.
Shugaba Pezeshkian ya kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi imanin cewa, kasashen yankin suna da karfin daukar matakai na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin, bisa tushen kyakkyawar makwabtaka da mutunta juna da kyautata mu’amala mai ma’ana, da share fagen kafa wani tsari na hadin gwiwa da taimakekkeniya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Shugaban kasar hadin gwiwa
এছাড়াও পড়ুন:
Iran da Masar sun tattauna kan rikicin da Isra’ila ta jefa yankin gabas ta tsakiya
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya yi kira ga kasashen duniya da su kawo karshen rikicin da Isra’ila ke ci gaba da haifarwa a yankin gabas ta tsakiya.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, Araghchi ya yi Allah wadai da sabbin hare-haren da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza tare da hana kai agajin jin kai a yankin a matsayin keta haddin yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta watan Janairu.
Ya kuma yi kira da a dauki matakin gaggawa a duniya kan yadda Isra’ila ke ci gaba da ruruta wutar rikici a yankin baki daya.
Isra’ila ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, amma ta kasa cimma manufofinta da ta ayyana kan yakin, duk da kashe Falasdinawa 50,000 galibi mata da kananan yara, tare da jikkata wasu fiye da 113,213.
Gwamnatin mamaya ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta amince da shirin tsagaita wuta da kungiyar gwagwarmayar Hamas a Gaza, wadda aka fara aiki da ita a ranar 19 ga watan Janairu.
Bayan shudewar watanni biyu da fara aiwatar da yarjejeniyar, Isra’ila ta sa kafa ta yi fatali da ita, kuma ta ci gaba da kaddamar da hare-haren kisan kiyashi a kan al’ummar Gaza