Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Kwalejin Koyon Tukin Jiragen Sama
Published: 19th, February 2025 GMT
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Dokta Danjuma Adamu Ismaila a matsayin shugaban kwalejin koyon tukin jiragen sama ta Najeriya (NCAT) da ke Zariya.
Sanarwar da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce Dakta Ismaila, kwararre kan harkokin sufurin jiragen sama, da manufofin tattalin arziki, ya kammala karatunsa na digiri a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya samu digiri a fannin kimiyyar lissafi a shekarar 1989.
Ya kuma yi babbar Difloma ta a fannin Sufuri sannan ya halarci kwasa-kwasan da dama, da tarukan karawa juna sani.
Hakazalika memba ne na kungiyar masana harkar sufurin jiragen sama ta Birtaniya, wato Aeronautical Society, UK, da Ƙungiyar Binciken Sufurin Jiragen Sama, da sauransu.
Kafin nadin nasa, Dr. Danjuma Adamu Ismail malami ne a jami’ar sufuri ta tarayya dake Daura.
Daga Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwalejin Koyon Tukin Jiragen Sama
এছাড়াও পড়ুন:
Kwana Daya Bayan Kwace Fadar Shugaban Kasa, Sojojin Sudan Sun Kwace Babban Bankin Kasar
A ci gaba da shimfida ikonsu da suke yi a cikin birnin Khartum, sojojin Sudan sun kwace iko da babban bankin kasar, kwana daya bayan da su ka kori dakarun kai daukin gaggawa daga fadar shugaban kasa.
Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya nakalto majiyar sojojin Sudan tana cewa; A yau Asabar sun yi nasarar kwace iko da babban bankin kasar, tare kuma da shimfida ikonsu a cikin wasu yankunan na birnin Khartum.
Kakakin sojan kasar Sudan Nabil Abdullah, ya bayyana cewa; Mun rusa sojoji da kayan aikin abokan gaba. Haka nan kuma Abdullah ya sanar da kwace wasu ma’aikatu da suke a tsakiyar birnin Beirut da su ka kasace a karkashin ikon dakarun kai daukin gaggawa.
Ana zargin rundunar kai daukin gaggawa da tafka laifukan yaki a cikin yankunan da a baya su ka shimfida ikonsu a ciki, har da babban birnin kasar Khartum.