Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-03-23@23:58:44 GMT

Matasan Jihar Jigawa Sun Karrama Gwamna Umar Namadi

Published: 20th, February 2025 GMT

Matasan Jihar Jigawa Sun Karrama Gwamna Umar Namadi

Gwamnatin Jihar Jigawa ta dauki matasa fiye da 6,000 aiki a fannoni daban-daban a fadin jihar, a kokarinta na ganin ta inganta rayuwarsu.

A saboda haka ne ma matasan da aka dauka aikin suka karrama Gwamnan Jihar, Malam Umar Namadi, bisa kokarinsa na samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin al’ummar jihar.

Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ruwaito cewa, taron karramawar, wanda aka gudanar a gidan Gwamnati dake Dutse Babban Birnin Jihar, ya hada da wadanda suka ci gajiyar shirye-shiryen gwamnati da suka hada da  J-Teach, da  J-Agro, da  J-Health, da  J-Millionaires, da sabbin likitocin da aka dauka aiki a bangaren lafiya.

A yayin taron, kowanne rukuni ya mika lambar yabo ga Gwamna Umar Namadi don nuna godiya bisa kokarinsa na ci gaban matasa tare da sharbar romon dimokradiyya.

A jawabin sa, Gwamna Umar Namadi ya nuna matukar farin cikinsa da wannan karramawar da matasan suka yi masa.

Yana mai cewar wannan girmamawar ba tasa ce kadai ba,  ta daukacin al’ummar Jihar Jigawa ce gaba daya ba shi kadai ba.

A don haka, ya yaba wa matasan bisa jajircewarsu wajen kafa kyakkyawar rayuwa nan gaba, da kuma taimakawa ci gaban al’umma.

Malam Umar Namadi, ya yi nuni da cewar, matasan Jigawa sun nuna kwarewa da kishin kasa wajen tabbatar da ci gaban jihar.

Yana mai cewar, shakka babu, da irin wannan himma da kwazon matasa, jihar za ta ci gaba da samun ci gaba a fannoni da dama.

Sai dai kuma, Namadi ya bukaci matasan da su ci gaba da kokari wajen bunkasa jihar, yana mai jaddada cewar ci gaban Jigawa na hannun al’ummarta.

Ya kuma tabbatar da kudirin gwamnatinsa na kara samar da damarmaki ga matasa, ta hanyar daukar aiki, da kuma bunkasa tattalin arziki, domin tabbatar da kyakkyawar makoma ga jihar.

Taron ya samu halartar Kakakin Majalisar dokokin Jihar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin da Sakataren Gwamnatin, Malam Bala Ibrahim da kwamishinoni da sauran jami’an gwamnatin Jihar.

 

Usman Mohammed Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa Umar Namadi

এছাড়াও পড়ুন:

Gobara ta tashi a gidan mai sakamakon fashewar tanka a Neja

Wata tanka ɗauke da man fetur ta kama da wuta yayin da ta ke sauke mai a gidan mai na A.A. Rano da ke Kontagora, a Jihar Neja.

Lamarin ya faru ne da da misalin ƙarfe 7 na daren ranar Lahadi kusa da Asibitin Gaba.

Gwamnonin Arewa sun yi wa Radda ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara

Shaidu sun ce gobarar ta fara ne yayin da ake sauke man fetur, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba kasancewar sauran tankunan mai maƙare suke da fetur.

Jami’an kashe gobara sun garzaya wajen don shawo kan lamarin, amma har yanzu wutar na ci gaba da yaɗuwa.

“Babu wanda aka ruwaito ya rasa ransa, amma mutane sun tsere domin tsira da rayukansu,” in ji wani mutum, mai suna Abba Mohammed.

Ƙoƙarin jin ta bakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, ya ci tura zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gobara ta tashi a gidan mai sakamakon fashewar tanka a Neja
  • Mahaifiyar Gwamnan Katsina ta rasu
  • Gwamnatin Jigawa Ta Nanata Dokar Haramta Kiwon Dare
  • Hikimar Gwamnatin Jihar Jigawa Na Kaddamar Da Shirin Gina Rijiyoyin Burtsatsan Noman Rani
  • GMBNI Ta Yi Allah-wadai Da Kisan Gillar Wani Almajiri A Jihar Jigawa
  • Dangote Zai Gina Sabuwar Masana’antar Siminti A Jihar Ogun
  • Dattawan Arewa sun buƙaci Tinubu ya dawo da Fubara kan kujerarsa
  • Sojoji sun ceto mutum 84 da ’yan bindiga suka sace a Katsina
  • Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna Ta Raba Abinci, Tufafi Ga Marayu, Mabukata Da Malamai
  • Gwamnatin Yobe na ciyar da almajirai a Tsangayu 85 kullum