NAJERIYA A YAU: Tanadin Dokar Kasa Kan Kirkirar Gwamnatin Bibiya A Kano
Published: 20th, February 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Tun bayan sanarwar shirin kafa gwamnatin bibiya ko kuma ‘shadow government’ a turance da wata kungiya ƙarƙashin Jam’iyyar APC a Jihar Kano tace za ta yi ne ne dai al’umma da dama ke ta jefa ayar tambaya kan halascinta.
Kungiyar dai ta bayyana cewa za ta kafa wannan gwamnati ne don bibiyan ayyukan gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf don tabbatar da ana abin da ya kamata.
Sai dai wannan sanarwa na ci gaba da yamutsa hazo inda wasu ke kallon halascin wannan gwamnati.
NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin AlbashiShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan halascin kafa gwamnatin bibiya a Jihar Kano.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnatin bibiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gaza: Sojojin HKI Sun Sake Kai Wa Asibitin “Ma’amadani Hari
Jiragen yakin HKI sun harba makamai masu linzami guda biyu akan ginin asibitin Ma’amadani dake Gaza. Harin ya yi sanadiyyar rushewar wasu bangarori da su ka hada dakunan yin gwaje-gwaje da kantin sayar da magani.
Saboda hare-haren na Isra’ila a wannan asibitin, da akwai gwamman marasa lafiya da suke kwance a kasa a waje, yayin da wasu kuma suke kwance wajen asibiti.
Kungiyar Hamas ta bayyana harin da sojojin HKI su ka kai wa asibitin da cewa wani sabon laifi ne na dabbanci da ‘yan sahayoniyar suka tafka a Gaza.
Haka nan kuma Kungiyar ta Hamas ta zargi Amurka da cewa ita ce take bai wa HKI haske akan tafka laifukan da take yi a Falasdinu.
Bugu da kari kungiyar ta Hamas ta kuma yi mamaki akan yadda kungiyoyin kasa da kasa da su ka hada da MDD suke yin shiru akan laifukan da ake tafkawa da ba su da tamka a wannan zamanin, akan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da cutar da marasa lafiya da korarsu daga asibiti zuwa kan tituna.