Kungiyoyin Falasdinawa A Gaza Sun Bukaci Yin Taron Musamman Domin Dakile Batun Tilasa Wa Mutanen Gaza Yin Hijira
Published: 20th, February 2025 GMT
Kungiyoyin Falasdina mabanbanta sun yi kira da a gudanar da taron musamman na al’ummar Falasdinu domin a tattauna hanyoyin da za a dakile batun tilastawa mutanen Gaza yin hijira.
Kungiyoyin na falasdinawa sun bayyana hakan ne dai a wani taro da su ka yi a Gaza domin karfafa gwiwar mutanen wannan zirin su ci gaba da jajurcewa da tsayin dakar da suke yi, tare da kara da cewa; Babu yadda za a yi al’ummar Falasdinu su fita daga kasarsu.
Mahalarta taron na Gaza sun bayyana furucin da shugaban kasar Amurka ya yi akan fitar da Falasdinawa daga Gaza da cewa yana nuni akan yadda Amurka da ‘yan sahayoniya su ka yi tarayya a laifukan da aka tafka akan Falasdinawa, haka nan ita kanta wannan maganar tana nufin shelanta wani sabon yakin akan al’ummar Falasdinu da hakan yake da bukatar fitar da wani matsayin na kasashen larabawa da kuma kungiyoyin kasa da kasa.
A karshe sun bukaci ganin cewa taron kasashen larabawa da za a yi nan gaba kadan, ya fito da wani tsari na ci gaban al’umma, saboda kawo karshe duk wani batu na yin hijira. Haka nan kuma sun bukaci ganin masu alaka da ‘yan mamaya daga cikin larabawa sun yanke ta.
Jami’in da yake kula da tuntubar juna a tsakanin kungiyoyi mabanbanta Khalid al-Badhash ya bayyana cewa; Duk da baranazar da hakkokin falasdinawa suke fuskanta, da kuma makirece-makircen Amurka, sai dai kuma batun kare hakkokin Falasdinawa ya sake dawowa da karfi a duniya, kuma duniyar ta gane hakikanin ‘yan mamaya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila ta yi barazanar fadada hare-hare Gaza yayin da ta yanke Rafah daga birnin Khan Yunis
Isra’ila ta ce ta karbe iko da wata muhimmiyar hanya a zirin Gaza a wani mataki da ya yanke gaba daya yankin kudancin Rafah mai yawan jama’a daga sauran yankunan Falasdinawa da aka yiwa kawanya.
A cikin wata sanarwa da Isra’ila ta fitar yau Asabar ta ce dakarunta sun yi wa Rafah kawanya gaba daya tare da samar da “yankin tsaro” a can.
Sanarwar da ministan harkokin soji na gwamnatin Isra’ila Katz ya fitar ta ce sojojin sun karbe ikon “Morag axis, wanda ke ratsa Gaza tsakanin Rafah da Khan Yunis.”
Katz ya kuma yi kira ga Falasdinawa da su fara kaura zuwa yamma, yana mai gargadin cewa nan ba da jimawa ba za a kara kaimi da fadada ayyukan soji zuwa wasu yankuna a cikin mafi yawancin Gaza.
IDF ta ce ta karɓe da abin da ta bayyana da cibiyar tsaronta da ta yi wa laƙabi da ”Lungun Morag”, sunan wani ginin da Isra’ila ta taɓa yi tsakanin biranen biyu.
A yanzu haka sojojin Isra’ila na gina titi a wurin, da nufin samar da wani wuri da Isra’ila ke iko da shi da ya raba Zirin Gaza.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Hamas ke cewa ta aika wakilanta zuwa Masar domin tattaunawa da masu shiga tsakani kan yiwuwar dawo da yarjejeniyar zaman lafiya.