Turkiya Ta Karbi Bakuncin Tattaunawar Sulhu Tsakanin Habasha Da Somaliya
Published: 20th, February 2025 GMT
An yi zaman farko na tattaunawar sulhu a tsakanin kasashen Habasha da Somaliya a birnin Ankara wanda kasar Turkiya take a matsayin mai shiga tsakani.
Ministan harkokin wajen kasar Turkiya Hakan fidan ya yi ganawa da daban-daban da ministocin harkokin wajen kasashen na Habasha da Somaliya.
Bayan wannan ganawar minstan harkokin wajen na Turkiya ya bayyana cewa; Yin aiki tare a tsakanin kasashen yankin yana da matukar muhimmanci a wannan zamanin da duniya take cike da sarkakiya.
Kamfanin dillancin labarun “Anatol” na Turkiya ya nakalto ministan harkokin wajen kasar yana yin ishara da babbar dama da aka samu a wannan lokacin domin ayyana makomar yankin na zirin Afirka, da kuma mayar da kalubalen da ake fuskanta ya zama wata dama
Minista Fidan ya kuma ce, tattaunawar da ake yi ba za ta takaita akan warare sabanin da yake a tsakanin kasashen na Habasha da Somaliya ba, zai zama mai wakiltar mahanga faffada ta siyasar nahiyar Afirka baki daya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Habasha da Somaliya harkokin wajen
এছাড়াও পড়ুন:
Aljeriya ta yi barazanar korar jami’an diflomasiyyar Faransa 12
Rikicin diflomasiyya tsakanin Paris da Algiers na dada kamari, inda Aljeriya ta bukaci wasu jami’an diflomasiyyar Faransa 12 da su fice daga kasar cikin sa’o’i 48.
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noël Barrot ya sanar cewa, Aljeriya ta bukaci jami’an diflomasiyyar Faransa da su fice daga kasar bayan kama wasu ‘yan kasar Aljeriya uku a Faransa.
“Ina kira ga hukumomin Aljeriya da su yi watsi da wannan matakin, inda ya kara da cewa: “Idan har aka ci gaba da yanke shawarar korar wakilanmu, ba mu da wani zabi illa mu mayar da martani cikin gaggawa.”
Shekaru da dama, alakar diflomatoyyar da ke tsakanin Aljeriya da Faransa ta yi tsami.
A farkon watan Afrilu, ministan harkokin wajen Faransa ya je kasar Aljeriya, domin kokarin warware matsalolin da suka jefa kasashen biyu cikin tabarbarewar diflomasiyya.
Bayan ganawa da shugaban kasar Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune, Jean-Noël Barrot ya bayyana muradin kasashen biyu na “sake gina dangantakar abokantaka.”
A daidai lokacin da ake fuskantar tsamin dangantaka tsakanin Algiers da Paris, ofishin mai gabatar da kara na Faransa ya tuhumi, wasu ‘yan kasar Aljeriya uku, a ranar 11 ga Afrilu, ciki har da wani jami’in ofishin jakadanci, da zarginsu da hannu a sace wani dan adawar gwamnatin Algeria, Amir Boukhors, da aka sani da “AmirDZ na Paris” a cikin 2024.
Aljeriya ta yi kakkausar suka a ranar Asabar, 12 ga Afrilu, don nuna adawa da kamawa da tsare daya daga cikin jami’an ofishin jakadancinta a kasar Faransa tare da neman a gaggauta sakin shi.