Dubban Falasdinawa Sun Kauracewa Gidajensu A Dai-Dai Lokacinta Sojojin HKI Suke Fafatawa Da Dakarun Falasdinawa
Published: 20th, February 2025 GMT
Dubban Falasdinawa ne suka kauracewa gidajensu a yankin yamma da kogin Jordan. Tun ranar 21 ga watan Jeneru na wannan shekara ta 2025, wato kwanaki biyu kacal da tsaida wuta a Gaza, sojojin HKI suka fadawa sansanin yan gudun hijira na Jenen inda suka fara fafatawa da dakarun Falasdinawa a yankin. Da nufin korarsu.
Dagan nan ne dubban Falasdinawa suka fara kauracewa gidajensu a yankin. Wasu suka dauki dukkan iyalansu su a mota su tafi inda ba’a tashin hankali. Wasu kuma sukan taka da kafafuwansu zuwa nesa daga inda ake fada da tashin hankali.
Wani dan agaji a yankin ya bayyana wa Jaridar ‘Arabsnews’ cewa bai taba ganin irin wannan kaurar da Falasdinawa suke yi ba, sai wanda aka yi a yakin 1967 inda falasdinawa 300,000 suka kauracewa gidajensu, sai kuma kafin haka a shekara ta 1948 falasdinawa 700,000 ne, sojojin yahudawan suka tilastawa falasdinawa kauracewa yankunansu a kasarsu da aka mamaye.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Kashe Mutane 7 A Yayin Da ‘Yan Ta’adda Suka Ƙaddamar Da Wani Sabon Hari A Adamawa
An tabbatar da mutuwar mutane bakwai a wani sabon harin da ‘yan ta’adda suka kai a kauyen Garaha Lar da ke jihar Adamawa. Shugaban karamar hukumar Hong, Honarabul Usman Wa’aganda ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa, wani mazaunin garin ya ɓata yayin da maharan suka lalata gidaje da kadarori. An Gudanar Da Harkokin Cudanya Da Musayar Al’adu Tsakanin Sin Da Malaysia A Birnin Kuala Lumpur Jigawa Za Ta Zama Cibiyar Binciken Lafiya Nan Ba Da Jimawa Ba – Gwamna Namadi Wa’aganda ya kuma bayyana cewa, wani Ɗan banga na yankin ya mutu bayan da wani bam ya tashi a lokacin da yake ƙoƙarin tabbatar da tsaron yankin. A cewarsa, motar ‘yansandan da ke sintiri ta ofishin ‘yansanda na Garaha ita ma ta ƙone yayin da wani abun fashewa ya fashe acikin motar amma babu wani mutum da ya rasa ransa. Shugaban ya ce, tsoron bama-baman da maharan ke amfani da su ya sanya zuwa wuraren da aka kai hare-haren ke da matukar wuya. Wa’aganda ya buƙaci a tura sojoji yankin da kuma tallafa wa waɗanda harin ya rutsa da su.Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp