Hamas Ta Ce Tana Iya Sakin Dukkan Fursinonin Yahudawa Gaba Daya A Lokaci Guda
Published: 20th, February 2025 GMT
Kungiya mai gwagwarmaya ta Falasdinawa Hamasa ta bayyana cewa tana iya sakin fursinoni yahudawa wadanda suke hannunta gaba daya a lokaci guda a marhala ta biyu ta musayar fursinoni tsakaninta da tare da sharadin ta cika al-kawulan da ta nauyi alhakin aiwatar da shi a wannan karon. Daga cikin har da maida tsagaita wutan na din din din
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Taher Al-Nounou ya cewa idan an yi haka za’a kammala musayar fursononin gaba daya, sannan HKI ta sake duk fursinonin falasdinawa gaba daya da suke hannunta.
Kafin wannan sanarwan dai ministan yaki na HKI Isarael Katz ya bayyana cewa HKI tana shirin shiga tattaunawa ba gaba ba kai tsaye ba, da Falasdinawa a marhala ta biyu da kungiyar Hamas, Ya kuma kara da cewa gwamnatinsa tana samun goyon bayan gwamnatin Amurka.
A zagaye na farko an musayar dai yahudawa 33 Hamas ta saka sannan Falasdinawa kimani 2000 suka sami yanci. Dakarun Qassam kadai ta saki yahudawa 19 a yayinda sauran kuma sauran kungiyoyin kuma sake sauran. A taunawa ta gaba ce za ta fayyace yadda tattaunawa ta gaba zata kasance.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Rantsar Da Sabbin Shugabannin Kungiyar Manyan Sakatarorin Jihar Zamfara
Kungiyar manyan sakatarorin ma’aikatun jihar Zamfara(ZASPEF) ta sha alwashin ci gaba da bayar da shawarwari don inganta iyyuka da sha’anin mulki.
Zababben shugaba Malam Yakubu Sani Haidara ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da su a matsayin sabbin shugabannin kungiyar a Gusau.
Yakubu Sani Haidara ya bayyana cewa, yayin da ma’aikatan gwamnati ke ci gaba da bunkasa, za su ci gaba da bayar da shawarwarin ci gaba da gudanar da shirye-shirye na inganta karfin harkokin mulki.
Shugaban ya bayyana cewa, wannan yunkurin zai sa a fi amfani da shawarwarin manyan Sakatarorin wajen tsara manufofi da aiwatar da su.
Sani Haidara ya kuma ce a matsayinsu na manyan masu gudanar da mulki, ya ba da tabbacin goyon bayansu ga gwamnati mai ci ta Gwamna Dauda Lawal.
A jawabinsa na bude taron, shugaban riko na kungiyar mai barin gado Muhammad Abubakar, ya ce sun yi aiki tukuru wajen ganin sun samar da fahimtar juna a tsakanin manyan sakatarorin da ya kai ga samar da wani gagarumin dandali da ke samar da hadin kai, da bayar da shawarwari da kuma kwarewa a aiki.
Ya bukaci sabbin shugabannin da su ci gaba da inganta ayyukan yi a jihar Zamfara.
Shi ma da yake jawabi, shugaban taron kuma shugaban hukumar ma’aikatan jihar Zamfara Alhaji Aliyu Muhammad Tukur, ya yi kira ga sabbin shugabannin kungiyar da su yi aiki tukuru domin tabbatar da amincewar da aka yi musu ta hanyar sadaukar da kai da kuma aiki da gaskiya.
Sabbin shugabannin kungiyar ta Zamfara State Permanent Secretaries’ Forum (ZASPEF) sun hada da Yakubu Sani Haidara a matsayin shugaba, da Dr. Barira Ibrahim Bagobiri mataimakiyar shugaba, da Shehu Baraya Gusau a matsayin ma’ajin kudin,
da Bashir Usman Salihu jami’in hulda da jama’a.
Yayin da sauran su ne Yazid Attahiru mai binciken kudi, da
Musa Garba Bukkuyum mai bada shawara kan harkokin shari’a,
da Garba Aliyu Gayari, a matsayin Sakatare.
Aminu Dalhatu