Hamas Za Ta Saki Dukkan Fursunonin Isra’ila Da Ke Hannunta
Published: 20th, February 2025 GMT
Hamas ta nuna shirin ta na sakin duk sauran fursunonin da take riƙe da su Gaza a cikin musanye guda cikin mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninnta da Isra’ila.
Babban Jami’in Hamas, Taher al-Nunu, ne ya bayyanawa masu shiga tsakani cewa ƙungiyar tana da niyyar sakin fursunonin gaba ɗaya maimakon rarraba su kashi-kashi kamar yadda aka yi a mataki na farko, wanda ya ce tabbaci ne da kuma shirinsu na ci gaba da warware batun.
A ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wutar na yanzu, an saki fursunonin Isra’ila 19 a madadin fiye da Falasdinawa 1,100 da ke gidajen yari, wanda a yanzu fursunoni 58 ne za su rage a Gaza, sannan ana shirin mayar da gawarwakin fursunoni takwas da suka mutu cikin matakai biyu.
Ana sa ran mataki na biyu na yarjejeniyar zai fayyace matakan da za a ɗauka domin cimma cikakken tsagaita wuta, inda ake shirin fara tattaunawa a wannan mako.
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Shirin Da’awah Na Mata A Jihar Jigawa
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya kaddamar da shirin Da’awah na mata a hukumance, domin karfafawa mata ilimin addinin musulunci, da karfafa alakar iyali, da kyautata rayuwa a tsakanin.
Da yake jawabi a wajen bikin a Dutse, Gwamna Namadi ya jaddada muhimmiyar rawar da mata ke takawa wajen tsara tarbiyar al’umma da kyawawan dabi’u.
“Kamar yadda aka sani, kusan rabin al’ummar jihar Jigawa mata ne, wadanda suka hada da iyayenmu, da ‘ya’yanmu, wanda hakan ya sa ya zama wajibi a kara zage dantse domin kula da addini da kuma tarbiyyarsu”.
Malam Umar Namadi ya jaddada wajibcin addini da ya rataya a wuyan maza na tallafa wa mata da bi da su hanyar shiriya, inda ya bukaci maza da su kyautata mata kamar yadda addini ya tanadar.
Ya kuma yabawa ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma ta jiha bisa jajircewarta wajen samun nasarar shirin, tare da yabawa babbar rawar da uwargidansa Hajiya Hadiza Umar Namadi ta taka wajen daukar nauyin shirin.
Namadi ya kuma yabawa Majalisar Malamai ta Jiha da dukkan masu ruwa da tsaki, bisa kokarin da suka yi wajen bunkasa tsarin da samar kayan aikin.
“Na yaba da kokari da sadaukarwar da kuka nuna wajen tabbatar da samun nasarar wannan shiri, Allah ya karbi dukkan gudunmawar da kuka bayar a matsayin Sadaqatul Jariyya.”
Ya kuma bukaci dukkan mahalarta taron da su rungumi shirin da zuciya daya, tare da jaddada muhimmancin ikhlasi, da kyawawan halaye, da hakuri da ayyukan Da’awah, tare da karfafa musu gwiwa da su rungumi koyarwar Alkur’ani mai girma.
Gwamnan ya kuma jaddada kudirin gwamnatinsa na tallafawa ci gaban mata, tare da yin kira ga shugabannin addini da na al’umma da su ci gaba da gudanar da shirin a dukkan kananan hukumomin jihar.
Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, shirin wanda hadin gwiwa ne tsakanin Gwamnatin Jihar Jigawa, Majalisar Malamai ta Jiha, da sauran shugabannin addini da na al’umma, na neman ilmantar da mata kan koyarwar addinin Musulunci, da inganta rawar da suke takawa wajen ci gaban iyali da ci gaban al’umma tare da samar da zaman lafiya, da kyautatawa da mutunta juna.
A karkashin shirin an zabo mata 574 daga sassa daban-daban na jihar.
Usman Muhammad Zaria