Aminiya:
2025-02-22@06:23:29 GMT

An haramta wa manyan tireloli aiki a Najeriya

Published: 20th, February 2025 GMT

Gwmanatin Tarayya ta haramta wa tireloli masu ɗaukar man fetur da nauyinsa ya kai lita 60,000 aiki a Najeriya daga ranar 1 ga watan Maris mai kamawa.

Hukumar Albarkatun Man Fetur ta Kasa (NMDPRA) ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne da nufin taƙaita yawan haɗuran tirelolin man fetur da ke sanadiyyar asarar ɗaruruwan rayuka da dukiyoyi na miliyoyin kuɗaɗe.

Hukumar ta ƙara da cewa zuwa ƙarshen wannan shekara ta 2025 za a haramta wa motoci masu ɗaukar man fetur lita 45,000 hawa titunan Najeriya.

Ta bayyana cewa bayan wani taron da aka gudanar kan yawan haɗuran tirelolin man fetur da irin asarar da hakan ke haifarwa, masu ruwa da tsaki a harkokin mai da sufuri hukumomin tsaro da sauransu sun yi ittifakin cewa a haramta wa tireloli masu ɗaukar man fetur da ya kai lita 60,000 hawa titi da kuma daukar mai a tashoshin sayar da man a faɗin Najeriya.

 

Ogbugo Ukoha, wanda shi ne Babban Daraktan Jigila na NMDPRA ya kara da cewar taron ya alaƙanta hatsarin motocin da nauyin kayan da motocin suke dauka kuma suka amince da ɗaukar matakin.

Ya bayyana cewa ƙaruwar hatsarin motocin musamman yadda ake samun asarar rayuka a lokacin da mutane ke zuwa kwasar man da ke tsiyaya.

Ukoha ya ce ganin yadda munin hatsarin ke ƙaruwa ya sa ɗaukar matakin ya zama dole.

Kungiyar NATO ta masu ababen haw ta koka da cewa matakin da gwamnati ta ɗauka zai jawo wa mambobinta asarar kimanin Naira biliyan 300.

Shugaban Ƙungiyar NATO, Yusuf Uthman, alaƙanta aukuwar haɗuran da rashin kyan hanyoyi da yanayin lafiyar motocin da kuma direbobi.

Ya ce mambobin kungiyar suna da tirela mai daukar lita 60,000 akalla guda 2,000 wadda kowacce kuɗinta ta kai Naira miliyan 150.

Don haka muddin aka hana motocin yin aiki to asarar da za su yi ta kai ta Naira biliyan 300.

Daga nan sai ya roki gwamnati ta shiga cikin lamarin ta hanyar saye motocin daga hannunsu domin rage musu raɗaɗi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Hatsari

এছাড়াও পড়ুন:

Wasu Motocin Bas-Bas Sun Tarwatse A Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Yankin Bat Yam A Kudancin Tel-Aviv

Motocin bas-bas guda uku sun tarwatse a birnin Tel Aviv, lamarin da ya haifar da rudani a tsakanin yahudawan sahayoniyya

Motocin bas-bas guda uku sun fashe da yammacin jiya Alhamis a wurare daban-daban a yankin Bat Yam da ke kudancin birnin Tel Aviv a tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila.

Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun bayyana cewa: Ma’aikatan tsaron cikin gidan haramtacciyar kasar Isra’ila ta “Shin Bet ta fara binciken wadanda ake zargin dasa ababen fashewa da suka yi sanadiyyar tarwatsewar motocin bas-bas din, kuma sun ba da rahoton zargin cewa; An samu wasu bama-bamai guda biyu wadanda ba su fashe ba.

Har ila yau, kafofin watsa labaran ‘yan mamayar sun ruwaito cewa: An dakatar da zirga-zirgan jiragen kasa gaba daya a yankin na Bat Yam sakamakon fashewar bama-baman, kuma Jami’an tsaro sun yi kira ga dukkan direbobi a yankin Tel Aviv da su duba motocin bas-bas dinsu, saboda tsoron ko an dasa bama-bamai a cikinsu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wasu sassan Abuja za su kasance cikin duhu a ƙarshen mako – TCN
  • INEC Ta Buƙaci Majalisa Ta kirkiro Dokar Hana ‘Yan Siyasa Zuwa Rumfunan Zabe Da Maƙudan Kuɗaɗe
  • Wasu Motocin Bas-Bas Sun Tarwatse A Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Yankin Bat Yam A Kudancin Tel-Aviv
  • An Haramta Wa Tankokin Man fetur Da Ke Jigilar Lita 60,000 Zirga-zirga A Faɗin Titunan Nijeriya 
  • Harin ’Yan bindiga: Mun yi asarar shanu sama da miliyan 4 – Miyetti Allah
  • Gwamnati Ta Haramtawa Tankokin Dakon Mai Ɗaukar Fiye Da Lita 60,000
  • Gwamnati Ta Haramtawa Tankokin Dakon Mai Ɗaukar Fiye Lita 60,000
  • Gwamnati Za Ta Haramta Amfani Da Tankoki Masu Ɗaukar Lita 60,000 Aiki Daga Maris 1
  • An Rantsar Da Sabbin Shugabannin Kungiyar Manyan Sakatarorin Jihar Zamfara