A wani ɓangare, an ware Naira biliyan 5.22 don gina gidaje 1,000 masu ɗaki biyu-biyu domin raba su kyauta ga waɗanda ambaliya ta shafa. Haka nan, an amince da Naira biliyan 9.76 don gina tituna bakwai da gyaran wasu a karkara

.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Gwamntin Waiting

এছাড়াও পড়ুন:

Jihar Kano Ta Samar Da Wani Salo Na Bunkasa Ilmin Addinin Musulunci A Jihar

Gwamnatin jihar Kano ta dauki wani gagarumin mataki na bunkasa ilimin addinin musulunci a jihar ta hanyar hada hannu da kungiyar Agaji ta Musulunci da ke Birtaniya,  wato Muslim Charity For United Kingdom a turance.

Wannan haɗin gwiwar na nufin tallafa wa makarantun Islamiyya da kayayyakin koyon  ilimi na zamani, da sauransu.

A cewar daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru, wannan shiri ya yi daidai da kokarin da gwamnati ke yi na karfafa fannin ilimi.

Haɗin gwiwar zai magance matsalolin da ke addabar ilimin addinin Islama, da tabbatar da cewa makarantun Islamiyya sun sami tallafin da ya dace don samu  ingantaccen yanayin karatu da koyarwa.

Ya yi nuni da cewa, Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dakta Ali Haruna Makoda, ya bayyana fatan cewa, wannan hadin gwiwa zai inganta ilimin addinin Musulunci, musamman a tsarin makarantun Islamiyya.

Ya ce, shirin zai mayar da hankali ne wajen samar da kayayyakin koyo na zamani domin inganta kwazon dalibai.

Da take jawabi a madadin tawagar, shugabar kungiyar agaji ta addininMusuluncida ke Birtaniya, Dr. Samira Abubakar Abdullahi, ta bayyana cewa kungiyar na aiki tukuru a Najeriya domin tallafawa harkokin ilimi da kiwon lafiya.

Ta bayyana cewa gudummawar da suke bayarwa sun hada da shirye-shiryen gyara makarantu, ayyukan ci gaban ilimi, da ayyukan kiwon lafiya.

“Mun zo  ma’aikatar don tattaunawa kan bangarorin haɗin gwiwa da kuma yi wa  kwamishina bayani game da ayyukanmu,” inji ta.

Kungiyar agajin tana aiki tukuru a Najeriya don tallafawa ayyukan ilimi da kiwon lafiya.

Daga Khadija Aliyu

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Yobe za ta gina gadar sama a kan N22.3bn
  • An tara Naira 16 a taron ƙaddamar da littafin IBB
  • Jihar Kano Ta Samar Da Wani Salo Na Bunkasa Ilmin Addinin Musulunci A Jihar
  • Dangote Ya Koma Matsayi Na 86 A Jadawalin Masu Arziƙin Duniya
  • NAJERIYA A YAU: Tanadin Dokar Kasa Kan Kirkirar Gwamnatin Bibiya A Kano
  • Gobara ta ƙone gidaje, dabobbi da kayan abinci a Kano
  • Kungiyar Hamas Ta Yi Watsi Da Karin Shuruddan Gwamnatin ‘Yan Sayoniyya Kan Tsagaita Bude Wuta
  • ’Yan bindiga sun Kashe mutum 2 kan jinkirin biyan kuɗin fansa
  • Gwamnatin Kano Ta Amince Da Biyan Bashin Albashin Ma’aikatan Tsaftar Muhalli 2,369