’Yan bindiga sun kashe mutum 12, sun sace wasu a Zariya
Published: 20th, February 2025 GMT
’Yan bindiga sun kashe wasu ’yan kasuwar Gwari 12, tare da sace wasu yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Zariya bayan cin kasuwa.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Tafoki da ke Jihar Katsina, bayan ’yan bindigar sun buɗe wa motarsu wuta.
An haramta wa manyan tireloli aiki a Najeriya Jami’an tsaron al’umma 6 sun mutu a artabu da ’yan bindiga a SakkwatoMasu sana’ar Gwari da abin ya shafa ’yan kasuwar Ɗan Magaji ne daga Ƙaramar Hukumar Zariya, a Jihar Kaduna.
Aminiya ta tattauna da wasu daga cikin waɗanda suka tsira, waɗanda suka ji raunuka, da kuma waɗanda aka sako bayan biyan kuɗin fansa Naira miliyan biyu.
Muhammad Zaharraddeen Sharaihu shi ne mutumin da ya kai wa ’yan bindigar kuɗin fansa domin a sako mahaifinsa da wasu mutum uku da aka yi garkuwa da su a dajin Katsina.
Zaharraddeen, ya ce tun yana kan hanya ‘yan bindigar suka riƙa kiran wayarsa har sai da ya isa inda suka ce ya tsaya.
Daga nan suka umarce shi da ya hau babur, sannan suka ce ya tsaya a wani waje don miƙa musu kuɗin.
Bayan ya miƙa kuɗin, wani mutum ya karɓa daga hannunsa, sannan aka umarce shi da ya koma bakin hanya ya jira fitowar ’yan uwansa.
A cewarsa, tun ƙarfe 1 na rana sai kusan Magariba aka sako mahaifinsa da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.
Mutum huɗu da aka biya miliyan biyu kafin a sako su sun haɗa da Malam Sharihu Umar Shehi, Malam Magaji Idris, Lawal Gambo Kwalano da Ida Ɗan Gwari
Lamarin ya ƙara dagula yanayin tsaro a yankin, inda jama’a ke fargabar ci gaba da ayyukan kasuwancinsu a yankunan da ke fama da hare-haren ’yan bindiga.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga yan kasuwa Garkuwa Gwari Zariya yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sun Kashe Mutane Fiye Da 400 A Yankin Al-Qatana Da Ke Jihar White Nile Ta Sudan
‘Yan tawayen Sudan na Dakarun Kai Daukin Gaggawa sun aikata muggan laifuffuka a yankin Al-Qatana da ke Jihar White Nile ta Sudan
Rahotonni sun bayyana cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan fararen hula a birnin Al-Qatana da ke arewacin jihar White Nile a Sudan, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan fararen hula tare da tarwatsa al’ummar yankin, inda suka fantsama zuwa gudun hijira.
Ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta tabbatar da cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun gudanar da wani kisan kiyashi da ya yi sanadin mutuwar mutane 433 a kauyukan birnin Al-Qatana na jihar White Nile.
Ma’aikatar harkokin wajen Sudan a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: Dakarun kai daukin gaggawa sun yi amfani da salon da suka saba yi na daukar fansa kan fararen hula da ba su dauke da makamai a kauyuka da kananan garuruwa bayan da suka sha kashi a hannun sojojin Sudan.