Majalisa ta fara bincike kan zargin USAID na tallafa wa Boko Haram
Published: 20th, February 2025 GMT
Majalisar Wakilai ta kafa kwamiti na musamman da zai binciki zargin da ake yi wa Hukumar Bayar da Agaji ta Ƙasa da Ƙasa ta Amurka (USAID), da tallafa wa Boko Haram.
An yanke wannan hukunci ne bayan ɗan majalisa, Inuwa Garba, ya gabatar da buƙatar gaggawa a zaman majalisar na ranar Alhamis.
’Yan bindiga sun kashe mutum 12, sun sace wasu a Zariya Hisbah ta rufe gidajen rawa a KatsinaGarba, ya nuna damuwa game da kalaman da ɗan majalisar dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi kwanan nan, inda ya zargi USAID da bai wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda, ciki har da Boko Haram tallafi.
Ya jaddada cewa Boko Haram ta haddasa babbar matsalar tsaro a Najeriya sama da shekara 10.
“Scott Perry ya yi wannan iƙirari a wani zaman majalisar dokokin Amurka, inda ya ce ana kashe sama da dala miliyan 697 duk shekara, kuma kai-tsaye ga ƙungiyoyi irin su ISIS, Al-Qaeda, da Boko Haram ne suke amfana,” in ji Garba.
“Boko Haram na da babbar maɓoya a Arewacin Najeriya, don haka akwai yiyuwar sun amfana da wannan tallafi.
“Idan zargin ya kasance gaskiya, hakan babbar barazana ce ga tsaron ƙasa da na duniya baki ɗaya,” in ji shi.
Bayan tattaunawa tsakanin ’yan majalisar, Kakakin Majalisar ya kafa kwamitin bincike na musamman don yin duba a kan lamarin.
Ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahotonsa cikin makonni biyu masu zuwa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram Ɗaukar Nawa Kwamiti Majalisar Wakilai
এছাড়াও পড়ুন:
An kama jarkokin manja maƙare da alburusai a Abuja
Rundunar ‘yan sandan Birnin Tarayya ta ce ta kama damin alburusai 488 da aka ɓoye a jarkar manja a tashar mota.
Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da ke kula da sintiri na musamman a Abuja, DCP Ishaku Sharu, ne ya bayyana hakan lokacin da yake holen wanda ake zargin a ofishin rundunar a ranar Litinin.
Matasa sun daka wawa kan kayan abincin da Seyi Tinubu zai raba a Gombe Gwamnonin PDP sun garzaya Kotun Ƙoli kan dakatar da Gwamnan RibasYa ce rundunar ta samu nasarar kama wanda ake zargin ne bisa tallafin wasu jami’an ƙungiyar masu sufurin motocin haya (NURTW).
Kazalika, ya ce sun kama wanda ake zargin ne ɗan asalin Jihar Katsina, ɗauke da harsashi 488 na bindigogin AK-47 da ya ɓoye a jarkokin manja.
DCP ya ce bayan rutsa shi ne ya bayyana musu cewa wani Yakubu Kacalla ne ɗan garin Funtua da ke Katsinan ya biya shi N100,000 domin karɓo masa kayan daga wajen wani mutum a Jihar Nasarawa.
Yanzu haka dai wanda ake zargin na hannun ‘yan sanda inda suke ci gaba da bincike domin kamo sauran masu hannu a safarar makaman.