Harin ’Yan bindiga: Mun yi asarar shanu sama da miliyan 4 – Miyetti Allah
Published: 20th, February 2025 GMT
Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta yi iƙirarin cewa wasu ’yan bindiga sun sace sama da shanu miliyan huɗu na mambobinta musamman a yankin Arewa maso Yamma.
Shugaban Ƙungiyar MACBAN na ƙasa, Baba Usman ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da sababbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙungiyar na jiha a Jihar Kebbi.
Ya ce, ɓarayin shanu na yawan kai wa Fulani makiyaya hari, lamarin da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.
Usman ya jaddada cewa, ana yawan sauya fahimtar Fulani makiyaya da kuma yin kuskuren sanya su a matsayin masu tayar da fitina, inda ya buƙaci jama’a su riƙa ganin su a matsayin ’yan Najeriya masu son zaman lafiya.
Ya kuma yi kira ga makiyaya da su guji shiga gonaki, su kuma zauna lafiya da manoma domin hana rikice-rikice.
Usman ya kuma yabawa gwamnatin tarayya da na jihohi bisa kafa ma’aikatar kiwo, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen magance matsalolin da makiyaya ke fuskanta.
Ya kuma yabawa gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris bisa ayyukan da suka inganta rayuwar al’ummar Fulani.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fulani makiyaya
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun ceto mutum 84 da ’yan bindiga suka sace a Katsina
Dakarun Sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 84 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Kankara a Jihar Katsina.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Nasir Mu’azu, ya bayyana cewa sojojin runduna ta 17 tare da tallafin jiragen yaƙi sun kai farmaki maɓoyar ’yan ta’adda da ke yankin Sanusi Dutsin-Ma da tsaunukan Pauwa.
’Yan bindiga sun sace shugaban kasuwar kayan miya ta Akinyele a Oyo Farashin fetur na iya tashi bayan Dangote ya daina sayar da mai a NairaYa ce a yayin farmakin dakarun sun kashe wasu daga cikin ’yan bindiga sannan suka kuɓutar da waɗanda aka sace.
Daga cikin mutanen da aka ceto, akwai maza bakwai, mata 23, da yara 54.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta yaba wa sojojin bisa ƙoƙarinsu, kuma tuni aka samar da abinci da kulawa ga mutanen da aka kuɓutar, kafin a mayar da su ga iyalansu.
Ya ƙara da cewa Gwamnatin Katsina ba za ta yi sulhu da ’yan ta’adda ba, domin tana da niyyar ci gaba da yaƙi da su har sai an daƙile matsalar garkuwa da mutane a jihar.