Na yi nadamar soke zaɓen 1993 — Babangida
Published: 20th, February 2025 GMT
Tsohon Shugaban Mulkin Soja na Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce ya yi nadamar soke zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993.
Ya ce da zai samu wata dama da zai yanke wani hukunci daban.
Harin ’Yan bindiga: Mun yi asarar shanu sama da miliyan 4 – Miyetti Allah Majalisa ta fara bincike kan zargin USAID na tallafa wa Boko HaramBabangida ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Alhamis, yayin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa mai suna ‘A Journey in Service’.
Yayin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ke nazarin littafin, Babangida ya amsa alhakin soke zaɓen da aka gudanar tsakanin Moshood Abiola na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) da Bashir Tofa na jam’iyyar National Republican Convention (NRC).
“Ina nadamar soke zaɓen ranar 12 ga watan Yuni. Na ɗauki alhakin matakin da aka ɗauka, domin hakan ya faru ne a ƙarƙashina ikona.
“Mun yi kuskure, kuma abubuwa sun faru cikin gaggawa,” in ji Babangida.
A baya, Babangida ya taɓa kare matakin soke zaɓen, inda ya ce an gudanar da shi cikin gaskiya da adalci, wanda a cewarsa Najeriya ba ta shirya karɓar mulkin dimokuraɗiyya ba a wancan lokaci.
“12 ga watan Yuni shi ne zaɓen mafi kyau a tarihin Najeriya—an yi shi cikin gaskiya da adalci. Amma abin takaici, dole muka soke shi.
“A lokacin, mun fahimci hatsarin miƙa mulki ga gwamnatin dimokuraɗiyya. Mun yi tsoron cewa idan muka miƙa mulki, cikin watanni shida, wani juyin mulki zai sake faruwa, kuma hakan zai zama gazawa a ɓangarenmu,” in ji shi.
Babangida, ya ƙara da cewa bayan soke zaɓen, gwamnatinsa ta shirya gudanar da wani sabon zaɓe a watan Nuwamban 1993.
Amma saboda tarzomar da ta biyo bayan soke zaɓen, ba a samu damar yin wani zaɓen ba.
A cewarsa a maimakon haka, sun kafa gwamnatin riƙon ƙwarya, amma daga baya, Janar Sani Abacha ya hamɓarar da ita.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Soke Zaɓe Zaɓen 1993 soke zaɓen
এছাড়াও পড়ুন:
Trump Ya Danganta Zelensky Da Dan Mulkin Kama Karya
Shugaban Amurka Donald Trump ya danganta takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky da “mai mulkin kama karya,” yana mai bukatarsa da ya gaggauta daukar matakin tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya da Rasha ko kuma ya yi kasadar rasa kasarsa.
Trump ya yi wadannan kalamai ne, kwana guda bayan da ya zargi Ukraine da haddasa yakin Rasha, yana mai cewa hakan ya janyo Washington cikin rikicin na shekaru uku.
An shirya wa’adin shekaru biyar na Zelensky zai kare a watan Mayun 2024, amma saboda dokar soja da aka kafa a watan Fabrairun 2022, ba za a iya gudanar da zabe ba.
Kalaman na Trump sun jawo martani cikin gaggawa daga jami’an Ukraine, inda ministan harkokin wajen kasar Andrii Sybiha ya jaddada cewa babu wanda zai tilasta wa kasarsa mika wuya. “Za mu kare hakkinmu na wanzuwa,” in ji shi a X.
A martanin da Zelensky ya mayar, ya zargi takwaransa na Amurka da rashin fahimtar Kremlin game da rikicin.
Bayan Kama mulki Trump, ya sauya manufofin Amurka kan Ukraine, inda ya kawo karshen yunkurin mayar da Rasha saniyar ware tare da yin shawarwari kai tsaye da shugaban Rasha Vladimir Putin.