NNPP ta rasa Ɗan Majalisa na farko da ya koma APC
Published: 20th, February 2025 GMT
Jam’iyyar adawa ta NNPP ta rasa ɗaya daga cikin mambobinta a Majalisar Wakilai zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Gwaram ta Jihar Jigawa, Yusuf Shitu Galambi. Shi ne ɗan jam’iyyar NNPP na farko da ya sauya sheƙa ya koma APC.
Na yi nadamar soke zaɓen 1993 — Babangida Hisbah ta rufe gidajen rawa a KatsinaIdan dai za a iya tunawa, ’yan jam’iyyar adawa na PDP da LP da dama sun sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.
Ɗan Majalisa Galambi ya bayyana cewa, ya bar jam’iyyar NNPP ne saboda rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar wanda ya haifar da wasu ƙararraki da suka shafi ayyukan jam’iyyar.
Ya kuma ƙara da cewa, Jam’iyyar NNPP ta rabu gida biyu sakamakon rigimar mulki tsakanin iyayen jam’iyyar da suka kafa ta, Sanata Rabi’u Musa Kwakwanso da ɗan takararta na Shugaban ƙasa a shekarar 2023, Peter Obi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwaram Jigawa Kwankwaso
এছাড়াও পড়ুন:
An Zabi ‘Yan Kasar Zimbabwe Kuma Mace Ta Farko A Matsayin Shugabar Shugabar Kwamitin Wasannin Olympic
‘Yar kasar ta Zimbabwe Kiristy Coventry ta zama mace ta farko daga fito daga nahiyar Afirka,kuma mace da za ta rike shugabannin hukumar wasannin Olympic.
An zabi Kirsty ‘yan shekaru 41 ne a yayin kada kuri’a ta sirri da aka yi da ‘yan takara 7 su ka yi gogayya. An yi zaben ne ne a yayin taron hukumar ta Olympic karo na 144, a birnin Costa, Navarino a kasar Greece a jiya 20 ga watan nan na Maris.
Gabanin zabenta dai , Kirsty ta kasance wacce ta zama gwarzuwa ta iyo har sau biyu a wasannin Olympic.
Za ta fara aikin nata ne na shugabancin hukumar wasannin Olympic a ranar 23 ga watan Yuni, da za ta gaji Thomas Bach dan kasar Jamus.