EFCC ta gargaɗi ciyamomi kan amfani da kuɗaɗen jama’a a Gombe
Published: 20th, February 2025 GMT
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta gargaɗi shugabannin ƙananan hukumomi da su guji almundahana tare da yin amfani da kuɗaɗen jama’a bisa gaskiya da adalci.
Shugaban EFCC, Mista Ola Olukoyede ne, ya bayyana haka yayin wani taro da aka shirya a Jihar Gombe kan ’yancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi.
A cewarsa, samun ‘yancin cin gashin kai ba yana nufin cewa shugabannin ƙananan hukumomi ba za a iya hukunta su ba idan sun aikata ba daidai ba.
“Shugabannin ƙananan hukumomi ba su da kariya a tsarin mulkin ƙasa. Idan aka samu rashin gaskiya wajen sarrafa kuɗaɗen jama’a, dole ne a ɗauki mataki,” in ji Olukoyede.
Ya kuma bayyana cewa EFCC za ta ƙara tura jami’anta zuwa Jihar Gombe domin sanya ido kan yadda ake sarrafa kuɗaɗen ƙananan hukumomi.
Har ila yau, Olukoyede ya yaba wa hukuncin Kotun Ƙoli da ya bai wa ƙananan hukumomi damar samun cikakken iko kan kuɗaɗensu, inda ya ce hakan zai taimaka wajen inganta ayyukan ci gaba.
Sai dai ya nuna damuwa kan yiwuwar wasu su karkatar da kuɗaɗen da aka ware don ayyukan al’umma.
Ya yi kira ga shugabannin ƙananan hukumomi da su bi doka wajen sarrafa kuɗaɗen jama’a.
“Ku tabbatar da gaskiya a dukkanin ayyukanku, ku kuma san dokokin da suka shafi amfani da kuɗaɗen jama’a. Rashin sanin doka ba hujja ba ce,” ya gargaɗe su.
Taron, wanda aka yi wa take da “’Yancin Cin Gashin Kai na Ƙananan Hukumomi: Samar da Ci Gaba Mai Ɗorewa,” ya mayar da hankali ne kan yadda ake iya amfani da kuɗaɗen jama’a ta hanyoyin da za su amfanar da al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gargaɗi Ƙananan Hukumomi amfani da kuɗaɗen jama a
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun ceto mutum 84 da ’yan bindiga suka sace a Katsina
Dakarun Sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 84 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Kankara a Jihar Katsina.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Nasir Mu’azu, ya bayyana cewa sojojin runduna ta 17 tare da tallafin jiragen yaƙi sun kai farmaki maɓoyar ’yan ta’adda da ke yankin Sanusi Dutsin-Ma da tsaunukan Pauwa.
’Yan bindiga sun sace shugaban kasuwar kayan miya ta Akinyele a Oyo Farashin fetur na iya tashi bayan Dangote ya daina sayar da mai a NairaYa ce a yayin farmakin dakarun sun kashe wasu daga cikin ’yan bindiga sannan suka kuɓutar da waɗanda aka sace.
Daga cikin mutanen da aka ceto, akwai maza bakwai, mata 23, da yara 54.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta yaba wa sojojin bisa ƙoƙarinsu, kuma tuni aka samar da abinci da kulawa ga mutanen da aka kuɓutar, kafin a mayar da su ga iyalansu.
Ya ƙara da cewa Gwamnatin Katsina ba za ta yi sulhu da ’yan ta’adda ba, domin tana da niyyar ci gaba da yaƙi da su har sai an daƙile matsalar garkuwa da mutane a jihar.