Leadership News Hausa:
2025-03-24@11:42:24 GMT

Wang Yi Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Uganda

Published: 20th, February 2025 GMT

Wang Yi Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Uganda

Ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Uganda Jeje Odongo a cibiyar MDD da ke birnin New York.

Yayin ganawar a ranar 18 ga wata, Wang Yi ya bayyana cewa, ana bukatar ra’ayin Afirka yayin da ake yada ra’ayin bangarori daban daban da kuma daidaita harkokin duniya baki daya.

Ya ce kasar Sin tana son hada hannu da kasashen Afirka wajen kafa tsarin daidaita harkokin duniya mai adalci da kuma samar da gudummawa wajen shimfida zaman lafiya da samun ci gaba a duniya. Wang Yi ya ce Sin tana yabawa kasar Uganda bisa muhimmiyar rawar da ta taka yayin da take shugabantar kungiyar kasashe ‘yan ba ruwanmu wato NAM, da taya ta murnar zama kasar da ta hada kan kasashen BRICS, haka kuma, Sin tana son yin kokari tare da kasar Uganda wajen sa kaimi ga hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa da tabbatar da adalci a duniya baki daya.

A nasa bangare, minista Odongo ya amince da tunanin girmama juna da tabbatar da ikon mallakar kasa da zaman daidaito da kuma adalci da kasar Sin da sauran kasashen BRICS suke bi, yana mai cewa kasarsa tana son yin kokari tare da kasashen BRICS da shiga bangare mai dacewa a duniya. (Zainab Zhang)

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: kasar Uganda

এছাড়াও পড়ুন:

Putin Ya Aike Wa Ayatullah Khamenei Da Murnar Idin Nowruz

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya mika sakon gaisuwar idin Nowruz na sabuwar shekarar hijira Shamsiyya ga jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan Nowruz, na  shigowar bazara da kuma sabuwar shekara ta Farisa.

Putin ya kuma aike da sakon fatan alheri ga shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, kamar yadda fadar Kremlin ta sanar a ranar Juma’a.

Nowruz, wanda ke nufin Sabuwar Rana, ita ce ranar farko ta watan Farvardin na kalandar Farisa. Ranar  a mafi yawan lokuta tana kamawa ne a ranar 20 ga Maris amma a duk bayan shekaru tana tana kamawa  daidai da 21 ga Maris.

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ranar Nowruz ta duniya a shekara ta 2010, inda ta bayyana ta a matsayin bikin bazara na kalandar Farisa, wanda aka shafe shekaru sama da 3,000 ana gudanar da ita.

Hakanan a cikin shekarar 2009, an sanya Nowruz a hukumance a cikin jerin abubuwa na tarihi da al’adu na bil adama na hukumar UNESCO.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran ta yi gargadin cewa keta hurumin Lebanon da Isra’ila ke yi barazana ne ga zaman lafiyar duniya
  • Ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falastinu a kasashen duniya
  • NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a harkokin kasuwanci
  • Firaministan Kasar Sin Ya Gana Da Sanata Steve Daines
  • Iran Ce Kasar Wacce Ta Fi Shigar Da Kayakin Kasuwanci Zuwa Kasar Afganistan A Shekarar Da Ta Gabata
  • Gwamnatin Kano Ga Ma’aikata: Duk Mai Bukatar Aikinsa Dole Ya Gabatar Da Kansa A Wajen Tantancewa
  • Amurka ta cire tukuicin wanda ya bayar da bayani kan mataimakin shugaban Taliban
  • Wang Yi: Kasar Sin Na Da Kwarin Gwiwa Kan Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Japan Da Koriya Ta Kudu  
  • Ranar Mata Ta Duniya: NPA Ta Mayar Da Hankali Wajen Kare ‘Yancin Mata –Dantsoho
  • Putin Ya Aike Wa Ayatullah Khamenei Da Murnar Idin Nowruz