Saudiyya ta Gayyaci Kasashen Larabawa Kan Batun Kan Batun Gaza
Published: 20th, February 2025 GMT
Saudiyya ta kira shugabannin kasashen Larabawa na yankin Gulf da kuma Masar da Jordan a wani taron domin tattauna batun Gaza.
Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ne ya gayyaci shugabannin a taron na gobe Juma’a, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyyar SPA ya ruwaito.
Kasashen Larabawa sun yi alkawarin yin aiki a kan wani shiri na bayan yakin Gaza da kuma sake gina Zirin a wani mataki na tunkarar shawarar shugaban Amurka Donald Trump na sake gina yankin da mayar da shi wurin shakatawa na gabar tekun kasa da kasa bayan korar mutanen Gaza zuwa wasu wurare.
Saudiyya ta ce taron na ranar Juma’a zai kasance ba na hukuma ba kuma za a yi shi ne cikin “tsarin dangantakar ‘yan’uwantaka da ke hada shugabannin,” in ji kamfanin SPA.
A cewar labarin, dangane da matakin da kasashen Larabawa suka dauka na hadin gwiwa da kuma shawarwarin da aka fitar dangane da shi, zai kasance cikin ajandar taron gaggawa na kasashen Larabawa da za a yi a Masar,” in ji SPA, yayin da yake magana kan shirin taron gaggawa na kasashen Larabawa da za a yi a ranar 4 ga watan Maris mai zuwa domin tattauna rikicin Isra’ila da Falasdinu.
Shi dai shugaban Amurka D.Trump ya yi kira ga kasashen Masar da Jordan su karbi Falasdinawa da ba su wajen zama bayan fitar da su daga Gaza, shawarar da kasashen suka yi fatali da ita.
Kasashen duniya da dama sun soki matakin na Trump, suna masu danganta shi da raba Falasdinawa da kasarsu ta gado.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasashen Larabawa
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Burkina Faso Ya Yi Fatali Da Tayin Saudiyya Na Gina Masallatai 200 A Kasarsa
Ya soki masu ra’ayin cewa dimukradiyya wani sharadi ne na ci gaba, yana mai cewa “karya ne” shi akwai wata kasa da ta ci gaba a karkashin tsarin dimukradiyya?.
Burkina24 ta nakalto cewa “Babu wata kasa da za a iya bayyanawa da ta ci gaba a dimukradiyya.
Ya ci gaba da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da sadarwa, bayyanawa, da kuma fahimtar da mutane mene ne juyin juya hali.
Traore ya yi fice wajen yanke shawarar ce bayan hayewarsa a matsayin shugaban kasar da ke yammacin Afirka.
Shugaban mai shekaru 37 da haihuwa wanda ya hau karagar mulki a watan Satumban 2022 ta hanyar juyin mulkin da ya hambarar da shugaban kasar na wucin gadi Paul-Henri Damiba kwanan nan ya yi watsi da tayin Saudiyya na gina masallatai 200 a kasarsa.
Ya bukaci kasar Musulunci da ta gwammace ta saka hannun jari a wasu muhimman ayyukan more rayuwa wadanda za su amfani al’ummarsa kai tsaye.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp