Aminiya:
2025-02-22@06:18:51 GMT

Ɗaliba ta rasu yayin da gini ya rufta a GGTC Potiskum

Published: 20th, February 2025 GMT

Wani ginin ajujuwa a Kwalejin ’Yan Mata ta Kimiyya da Fasaha (GGTC) Potiskum ya rufta, inda daliba ɗaya ta rasu kuma wasu da dama suka jikkata.

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da ɗalibai ke tsaka da karatu.

An rufe Jami’ar Kogi saboda zanga-zangar ɗalibai EFCC ta gargaɗi ciyamomi kan amfani da kuɗaɗen jama’a a Gombe

Gini ya faɗa kansu ne ba zato ba tsammani, lamarin ya haddasa mummunan tashin hankali tare da jefa ɗalibai da dama cikin baraguzan gini.

Bayan aukuwar lamarin, an yi gaggawar ceto ɗaliban, inda aka garzaya da su zuwa Asibitin Ƙwararru na Potiskum domin ba su kulawa.

Duk da an samu nasarar ceto da dama daga cikinsu, wata ɗaliba ta rasa ranta sakamakon raunukan da ta samu.

Tuni Kwamishinan Ilimi a matakin Farko da Sakandare, Farfesa Abba Idris Adam, tare da Sakataren Zartarwa na Hukumar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Yobe, Dokta Dauda Atiyaye, suka ziyarci wajen da lamarin ya faru, da kuma asibitin da ake kula da ɗaliban da suka jikkata.

Har yanzu ba a bayyana abin da ya yi sanadin rushewar ginin ba.

Amma hukumomi na ci gaba da bincike don gano haƙiƙanin dalilin aukuwar iftila’in.

Garin Potiskum na da nisan kilomita 100 daga Damaturu, Babban Birnin Jihar Yobe.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan mata Ɗaliba Ɗalibai karatu rasuwa

এছাড়াও পড়ুন:

An rufe Jami’ar Kogi saboda zanga-zangar ɗalibai

Hukumomin Jami’ar Tarayya da ke Lokoja a Jihar Kogi, sun rufe jami’ar har zuwa wani lokaci domin daƙile ci gaba da asarar rayuka da dukiya.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun magatakarda kuma sakatariyar majalisar Jami’ar, Dokta Rebecca Aimiohu Okojie, a ranar Alhamis kuma ta bayyanawa manema labarai a Lokoja.

Jihar Gombe na ƙarfafa haƙƙoƙin yara masu nakasa — Ƙungiyar JONAPWD NNPP ta rasa Ɗan Majalisa na farko da ya koma APC

Hukumar Jami’ar ta yi zargin cewa, ɗaliban sun tare babbar ƙofar shiga jami’ar ne tun bayan haɗarin da ya yi sanadin mutuwar ɗaliban jami’ar biyar a ranar Litinin, wanda ya sa shiga harabar jami’ar ke da wuya.

“Rufewar jami’ar ya biyo bayan asarar rayuka da ɗalibai biyar suka yi a wani mummunan haɗarin tirela a Felele, ranar Litinin 17 ga Fabrairu, 2025.

“Tun faruwar lamarin, ɗalibai sun tare ƙofar jami’ar duk da kakkausar murya daga gwamnatin jihar da kuma ƙoƙarin da hukumomin jami’ar suka yi na a kwantar da hankula.

“Saboda haka, bisa shawarar hukumomin tsaro na jihar da kuma daƙile ci gaba da asarar rayuka da dukiya, shugaban jami’ar bayan shawarwarin hukumar ta yanke, shawarar a madadin majalisar jami’ar cewa jami’ar, jami’ar da rassanta za a rufe su har sai baba-ta-gani. Ɗalibai za su bar wuraren karatu kafin ƙarfe 12 na rana ranar Alhamis, 20 ga Fabrairu.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsarin Fansho Na Jihar Jigawa Ya Yi Wa Sauran Jihohi Zarra- Premium Pension
  • Jami’an Diblomasiyya Daga Kungiyar G20 Da Dama Sun Isa Afrika Ta Kudu
  • Shirin Rigakafin Cututtuka Na UNICEF/GAVI Ya Sami Cikakken Hadin Kan Gwamnatin Jihar Jigawa
  • Shugaba Tinubu Ya Yaba Da Gudunmawar Da IBB Ya Bayar Yayin Mulkinsa
  • An rufe Jami’ar Kogi saboda zanga-zangar ɗalibai
  • Yanzu-yanzu: Gini Ya Rufta Wa Ɗaliban GGTC Potiskum
  • ’Yan bindiga sun Kashe mutum 2 kan jinkirin biyan kuɗin fansa
  • Rayuka 10 da dukiyar N11bn sun salwanta yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a Kano
  • Mutum 10 sun rasu, an lalata dukiyar N11bn yayin zanga-zangar yunwa a Kano — Rahoto