Kasar Sin Ta Kammala Hako Rijiyar Fetur Mafi Zurfi A Yankin Asiya
Published: 20th, February 2025 GMT
Kamfanin mai na kasar Sin (CNPC) ya sanar a yau Alhamis cewa, ya kammala aikin hakar rijiyar man fetur mafi zurfi a yankin Asiya, yayin da rijiyar ta kai zurfin mita 10,910 a hamadar arewa maso yammacin kasar Sin.
Rijiyar wacce aka fi sani da “Shenditake 1” da ke tsakiyar hamadar Taklimakan a cikin kwarin Tarim, a jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur, ta kasance wani gagarumin aiki na binciken kimiyya.
A cewar kamfanin CNPC, an fara aikin hakar rijiyar ne a ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2023, inda aka shafe fiye da kwanaki 580 kafin a kai ga kammala tsawon mita 10,910 na hakar, kana an shafe fiye da rabin lokacin, watau kimanin kwanaki 300 ana fama da aikin hakar tsawon mita 910 na karshe. Rijiyar ta ratsa cikin siffofin yanayin kasa har guda 12, wadda daga karshe ta kai ga isa shimfidadden dutsen da adadin shekarun samuwarsa suka kai tsawon shekaru miliyan 500. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
এছাড়াও পড়ুন:
Hikimar Gwamnatin Jihar Jigawa Na Kaddamar Da Shirin Gina Rijiyoyin Burtsatsan Noman Rani
An ruwaito cewa, shirin aikin noman ranin da aka kaddamar a yankin na Lallashi, zai karade hekta 10, wanda kuma sama da kananan manoma 80, za su amfana da shirin kai tsaye.
Bugu da kari, shirin zai taimaka wajen kara samar da girbin amfanin gona mai yawan gaske tare kuma da kara bunkasa tattalin arzikin jihar baki-daya.
Malam Aliyu Musa, da yake yin jawabi a madadin sauran manoman da ke yankin ya bayyana cewa, samar da shirin a yankin da gwamnatin jihar ta yi, tamkar zuba hannun jari ne.
A cewarsa, al’ummar yankin za su ci gaba da yin addu’a, domin shirin ya dore tare kuma da ganin an kara fadada shi, don su ma sauran yankunan jihar su amfana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp