‘Yansanda Sun Kwato Motoci 7 Da Aka Sace Da Taimakon Na’urar e-CMR A Kano
Published: 21st, February 2025 GMT
Ya ce, motocin da aka kwato sun hada da wata farar mota kirar Howo, wacce aka sace daga Riruwai, karamar hukumar Doguwa, Kano, a ranar 17 ga watan Janairu, 2025, aka kuma gano ta a Lokoja, jihar Kogi.
Akwai wata bakar mota kirar Honda Accord 2013, wacce aka sace daga Abuja ranar 18 ga watan Janairu, 2025, aka gano ta a filin jirgin sama na Kano.
Bugu da kari, akwai wata farar mota kirar Mercedes Benz GLK wacce aka sace a hanyar Magwan Kano a ranar 27 ga watan Janairu, 2025, aka gano ta a Hotoro Quarters Kano da wata jar Toyota Corolla LE da aka sace a Abuja a ranar 30 ga Janairu, 2025, aka gano ta a Kano.
Daya kuma wata bakar mota kirar Toyota Camry, wacce aka sace a Kaduna ranar 27 ga watan Janairu, 2025, aka gano ta a Kano.
Akwai Wata farar Toyota Hilux da aka sace daga Katsina a ranar 15 ga Fabrairu, 2025, aka same ta a Ring Road Bypass, Kano.
Har ila yau, akwai wata bakar mota ash mai suna Pontiac Vibe, wacce aka sace daga Katsina a ranar 15 ga Fabrairu, 2025, kuma aka gano ta a Ring Road Bypass, Kano.
Rundunar ‘yansandan ta jaddada mahimmancin rajistar motoci a na’urar e-CMR wajen bin diddigin motocin da aka sace, inda ta bukaci masu abin hawa da su yi rajista ta shafin https://cmris.npf.gov.ng don inganta tsaro.
Rundunar ta kuma ja hankalin jama’a da su kasance cikin taka-tsan-tsan tare da bayar da rahoton duk wani abu da suka shakku akai.
কীওয়ার্ড: ga watan Janairu wacce aka sace
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Fansho Na FRCN Da NTA Sun Yabawa Gwamnati Bisa Amincewa Da Biyan Harkokinsu
Ma’aikatan Gidan Rediyon Tarayya (FRCN) da na Hukumar Gidan Talabijin ta Najeriya (NTA) da suka yi ritaya, sun bayyana jin dadinsu kan karin haske da Ministar Kudi ta yi game da wadanda za su ci gajiyar Naira Biliyan 758 da aka amince da su don biyansu kudaden fansho da suke bi.
A tsokacin da suka yi game da lamarin a Kaduna, ’yan fanshon sun bayyana cewa, bayanin ya tabbatar da cewa za a raba kudaden ne zuwa sassa biyu na ma’aikatan da suka yi ritaya a karkashin hukumar fansho ta PTAD da kuma shirin bayar da gudunmawar fansho (CPS).
Sun bayyana fatan cewa za a biya kudaden kafin karshen watan da ake ciki, domin baiwa ‘yan fansho damar gudanar da azumin watan Ramadan cikin kwanciyar hankali da walwala.
Tsohon babban jami’in tsaro na NTA, Alhaji Abdullahi Umar, ya yabawa gwamnatin tarayya bisa wannan tabbacin da ta bayar, ya kuma bukaci kungiyoyin ‘yan fansho da su sanya ido sosai kan yadda ake biyan kudaden domin kaucewa duk wata matsala.
Ya kuma yi kira da a saka ‘yan fansho a cikin shirin inshorar lafiya na kasa (NHIS), wanda a baya aka dawo da shi, domin a taimaka musu wajen kula da lafiyarsu.
Suleiman Kaura