Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sun Kashe Mutane Fiye Da 400 A Yankin Al-Qatana Da Ke Jihar White Nile Ta Sudan
Published: 21st, February 2025 GMT
‘Yan tawayen Sudan na Dakarun Kai Daukin Gaggawa sun aikata muggan laifuffuka a yankin Al-Qatana da ke Jihar White Nile ta Sudan
Rahotonni sun bayyana cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan fararen hula a birnin Al-Qatana da ke arewacin jihar White Nile a Sudan, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan fararen hula tare da tarwatsa al’ummar yankin, inda suka fantsama zuwa gudun hijira.
Ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta tabbatar da cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun gudanar da wani kisan kiyashi da ya yi sanadin mutuwar mutane 433 a kauyukan birnin Al-Qatana na jihar White Nile.
Ma’aikatar harkokin wajen Sudan a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: Dakarun kai daukin gaggawa sun yi amfani da salon da suka saba yi na daukar fansa kan fararen hula da ba su dauke da makamai a kauyuka da kananan garuruwa bayan da suka sha kashi a hannun sojojin Sudan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gidauniyar Tunawa Da Sir Ahmadu Bello Za Ta Gudanar Da Taronta Karo Na 11 A Bauchi.
Gidauniyar Tunawa Da Sir Ahmadu Bello Za Ta Gudanar Da Taronta Karo Na 11 A Bauchi.Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta sanar da cewa za ta gudanar da bikin tunawa da Sir Ahmadu Bello na shekara karo na 11 a ranar Litinin, 24 ga Fabrairu, 2025, a Bauchi, Jihar Bauchi.
Taron, wanda aka shirya tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Bauchi, zai girmama marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato kuma Firaministan tsohuwar Yankin Arewa.
A bana, taken laccar shi ne “Arzikin Halitta: Juya Albarkatun Yankin Arewa Zuwa Ci Gaban Tattalin Arziki Mai Dorewa.”
Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan yadda za a yi amfani da albarkatun noma da ma’adanai da ruwa don bunkasa ci gaban tattalin arzikin yankin.
Duba da kalubalen tattalin arzikin da Najeriya ke fuskanta, musamman yankin Arewa, laccar za ta bayyana rawar da gwamnati da ɓangarori masu zaman kansu da kungiyoyin al’umma za su taka wajen inganta sarrafa albarkatu da bunkasa darajar kayayyaki da samar da ayyukan yi.
Babbar lacca za a gabatar da ita ne daga bakin Dr. Mansur Mukhtar (Sarkin Bai Kano), tsohon Mataimakin Shugaban Bankin Musulunci kuma Shugaban Bankin Masana’antu na Najeriya.
Ana sa ran Sanata George Akume, Sakataren Gwamnatin Tarayya, zai kasance Babban Bako na Musamman a wurin taron.
Haka nan, ana sa ran halartar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, kuma zai jagoranci taron.
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, zai kasance Babban Mai Masaukin baki. Haka kuma, ana sa ran halartar gwamnonin jihohi da ministoci da ‘yan majalisa da sarakuna da sauran manyan baki daga sassa daban-daban.
A cewar Darakta-Janar na Gidauniyar, Injiniya Dr Abubakar Gambo Umar, albarkatun yankin Arewa na da babban damar sauya tattalin arzikin yankin.
“Sai dai dole mu dauki matakan da za su tabbatar da sarrafa albarkatunmu cikin adalci da dorewa, domin amfanin kowa da kowa,” in ji shi.
A yayin taron, gidauniyar za ta bayar da tallafin karatu ga dalibai marasa galihu daga Jihar Bauchi da ke karatu a manyan makarantu domin tallafa musu.
Bugu da kari, za a karrama wasu fitattun mutane da lambar yabo saboda gudunmawar da suka bayar ga cigaban al’umma.
Har ila yau, za a gudanar da shirin ba da agajin lafiya domin samar da hidimar kiwon lafiya ga al’ummar yankin.
Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello an kafa ta ne domin ci gaba da girmama gadon shugabanci da ilimi da ci gaban tattalin arziki da marigayi Sardaunan Sakkwato ya assasa.
Bikin tunawa na kowace shekara, wanda ke gudana a jihohi 19 na Arewa, na zama wata kafa ta tattaunawa kan ci gaban yankin da shugabanci.
Gidauniyar ta nemi afuwar duk wani rashin jin dadi da sauya ranar taron ka iya haifarwa, tare da gode wa duk masu mara mata baya.
Rel: Khadija Kubau