Wasu Motocin Bas-Bas Sun Tarwatse A Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Yankin Bat Yam A Kudancin Tel-Aviv
Published: 21st, February 2025 GMT
Motocin bas-bas guda uku sun tarwatse a birnin Tel Aviv, lamarin da ya haifar da rudani a tsakanin yahudawan sahayoniyya
Motocin bas-bas guda uku sun fashe da yammacin jiya Alhamis a wurare daban-daban a yankin Bat Yam da ke kudancin birnin Tel Aviv a tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila.
Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun bayyana cewa: Ma’aikatan tsaron cikin gidan haramtacciyar kasar Isra’ila ta “Shin Bet ta fara binciken wadanda ake zargin dasa ababen fashewa da suka yi sanadiyyar tarwatsewar motocin bas-bas din, kuma sun ba da rahoton zargin cewa; An samu wasu bama-bamai guda biyu wadanda ba su fashe ba.
Har ila yau, kafofin watsa labaran ‘yan mamayar sun ruwaito cewa: An dakatar da zirga-zirgan jiragen kasa gaba daya a yankin na Bat Yam sakamakon fashewar bama-baman, kuma Jami’an tsaro sun yi kira ga dukkan direbobi a yankin Tel Aviv da su duba motocin bas-bas dinsu, saboda tsoron ko an dasa bama-bamai a cikinsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun Kashe mutum 2, sun sace manoma 10 a Neja
’Yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin awon gaba da aƙalla wasu 10 a hare-haren da suka kai Ƙananan Hukumomin Wushishi da Rafi a Jihar Neja.
Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa waɗanda aka kashe sun haɗa da ɗan sa-kai da wani mutum mai saran itace.
Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan Tsaro Rayuka 10 da dukiyar N11bn sun salwanta yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a KanoHar ila yau, ya ce wani ɗan sa-kai na daga cikin waɗanda aka sace.
“A halin yanzu, ’yan bindiga suna cikin dajin Akare. Sun sace ɗaya daga cikin ‘yan sa-kai, kuma yana da bindigogi biyu a tare da shi lokacin da suka yi awon gaba da shi.
“Ba mu san abin da za mu yi a yanzu ba. Mun shafe tsawon ranar ɗaya muna fafatawa da su. An kashe ɗaya daga cikin ’yan sa-kai da kuma wani mai saran itace,” in ji shi.
Mazauna yankin sun bayyana cewa har kawo hanzu ’yan bindigar suna cikin dajin tare da shanun da suka sace a yankin.
An ruwaito cewa sun kama mai saran itacen, tare da tilasta masa ya nuna musu hanya, sannan suka harbe shi.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa jami’an tsaro da ’yan sa-kai na ci gaba da ƙoƙarin bin sahun ‘yan bindigar.
Wani mazaunin yankin ya ce, “Mun ga ’yan bindigar suna tafiya da babura, uku-uku a kan kowanne.
“Suna wucewa ta wajen da suka saba bi a Kundu, a Ƙaramar Hukumar Rafi, sun nufin Ƙaramar Hukumar Mashegu tare da shanun da suka sace.”
Wani mazaunin Ƙaramar Hukumar Rafi, ya ce ’yan bindigar sun kuma kai hari wasu ƙauyuka a gundumar Gunna da safiyar ranar Laraba, inda suka ƙone rumbunan doya.
Da yake tabbatar da harin, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed (mai ritaya), ya ce, an tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin.
“An riga an tura jami’an tsaro zuwa yankin, kuma suna bin sahun ’yan bindigar.”