Babban Kwamandan IRGC Ya Bayyana Cewa: Amurka Da Isra’ila Ba Su Yi Nasara A Yakin Gaza Ba
Published: 21st, February 2025 GMT
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Amurka da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya ba su yi nasara a yakin da suka kaddamar kan ‘yan gwagwarmaya a Gaza ba
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Hossein Salami ya jaddada cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta samu wanzuwa idan babu Amurka, yana mai cewa, ita kanta Amurka ta kama hanyar rugujewa.
A yayin ganawarsa da Ziyad al-Nakhala babban sakataren kungiyar Jihadul-Islami, Manjo Janar Salami ya yi nuni da irin nasarorin da dakarun gwagwarmayar Falastinawa da al’ummar Gaza suka samu a kan yahudawan sahyoniya ‘yan mamaya, yana mai bayyana wannan nasara a matsayin nasara da take a fili kuma nasara ce bayyananniya ta Ubangiji” wacce ta kawo abin alfahari ga duniyar Musulunci, yayin da Allah ya girmama Falastinawa da nasara bayan tsawon shekaru ana killace da su saboda matakan zalunci.
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musuluncin ya kara da cewa: Zafin zalunci da wahalhalun da al’ummar Falastinu suke sha yana damun kowa a cikin zukata duk jurewa hakan yana da wahala da wuya, amma al’umma tana godiya ga Allah kasancewa wadannan al’amura sun kare da nasarar da jarumai a Gaza suka samu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jiragen Saman Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Luguden Wuta Kan Asibitin Baptist Da Ke Gaza
Jiragen saman yakin mamayar Isra’ila sun kai farmaki kan asibitin Baptist da ke birnin Gaza, lamarin da ya janyo dakatar da aiki a cikinsa
Wakilin gidan talabijin na Al-Alam Mohammed Al-Balbisi ya ruwaito cewa: Jiragen saman yakin sojojin mamayar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a wasu gine-gine na asibitin Baptist, da suka hada da ginin sashin kula da marasa lafiya cikin gaggawa da kuma motocin daukar marasa lafiya da wasu sassa da tantuna da ke ba da hidima ga wadanda suka jikkata.
Ya yi nuni da cewa da sanyin Safiya yau Lahadi, sojojin mamayar Isra’ila sun harba makamai masu linzami da dama kan wadannan gine-gine lamarin da ya tilastawa marasa lafiya da likitoci ficewa daga asibitin tare da fakewa a nesa da asibitin, inda hare-haren suka rusa gine-ginen asibitin.
Wakilin ya kara da cewa: Wannan shi ne karo na biyu da ake kai wa asibitin Arab Baptist hari, domin an kai harin bama-bamai a farkon fara kai hari kan Gaza, wanda ya yi sanadin mummunan kisan kiyashi da ya ci rayukan daruruwan mutane.