Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Cewa: Suke Da Hakkin Yanke Shawarar Makomar Kaarsu Ba Amurka Ba
Published: 21st, February 2025 GMT
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Iran ce zata yanke shawara a nan gaba kan matsayin kasarta, ba Trump ba
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a yammacin jiya Alhamis ya jaddada cewa: Iran ce take da hakkin yanke shawara kan makomarta ba Trump ba, yana mai jaddada wajabcin sauya ra’ayi domin dakile duk wani takunkumin da Trump ya kakabawa kasarsa.
A jawabin da shugaba Pezeshkian ya gabatar a wajen taron shugabannin lardin Tehran ta yamma da majalisar gudanarwa ta garuruwan Mallard, Shahriar da Quds, shugaba Pezeshkian ya bayyana cewa, ma’anar gudanarwa ita ce sanin damammaki da barazana a ciki da wajen kasar da kuma sanin irin karfi da ake da shi.
Shugaban kasar ya jaddada cewa: Trump na fadin wani abu, kuma wasu mutane sun saba da abin da Trump yake so. Mene ne Trump yake son aikatawa? A nan mu ne za mu yanke shawarar yadda za mu tafiyar da makomarmu. Idan ba Iran ba ta canza ra’ayinta ba, to, ta sanya wa kanta takunkumi a hukumance, amma idan ta sauya ra’ayinta, Trump ba zai kai ma burinsa ba, kuma komai yawan takunkumin da zai Sanya kan kasar Iran.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Shugaban kasar
এছাড়াও পড়ুন:
Palasdinawa Ne Zasu Fayyanace Makomarsu Ba Wasu Dan Mulkin Mallaka Ba: Qalibof
Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof ya bayyana cewa falasdinawa masu kasa ne zasu fayyace makomar kasarsu, don haka shirin da wasu manya-manyan kasashen duniya suke dashi a kan makomar Falasdinu da Falasdinawa ba dai-dai bane kuma zamu yi yaki da shi.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Teran ta nakalto shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammada Bakir Qolibft yana fadar haka a taron shuwagabannin majalisun dokoki na kasashen Asia a birnin Baku na kasar Azaibaijan.
Qolibof ya kuma kara da cewa shirin shugaban kasar Amurka yake yi na kwace gaza da kuma inda za’a maida Falasdinawa ba zai kai ga nasara ba.
Qalibof ya yi allawadai wadai da shugaba Trump kan shishigin da yake yi a cikin al-amuran Falasdinawa, da kuma yin watsi da kokarin Falasdinawa a gaza suke yi don kwato kasarsu.
Ya ce Iran ba za ta amince da duk wata kasa mai jin tana da karfi wacce za ta dorawa falasdinawa tunaninsa ba.
Shugaban majalisar ya bayyana cewa yakin da HKI ta fafata da falasdinawa a Gaza, da kuma kungiyar Hizbulla a kasar Lebanon, sun bayyana raunin HKI a fili, wannan duk tare da dukkan tallafin da take samu daga kasashen yamma musamman Amurka.
Daga karshe ya ce dole ne a sami yentacciyar kasar Palasdinu mai zaman kanta nan gaba.