INEC Ta Buƙaci Majalisa Ta kirkiro Dokar Hana ‘Yan Siyasa Zuwa Rumfunan Zabe Da Maƙudan Kuɗaɗe
Published: 21st, February 2025 GMT
Domin magance wannan kalubale, Muhammed ya ba da shawarar ka da a bar mutane su dauki kudi fiye da naira 50,000 a rumfunan zabe.
“Sayen kuri’u na daya daga cikin manyan barazana ga sahihin zabe a Nijeriya. Muna bukatar dokar da ba wai kawai ta haramta wannan dabi’ar ba har ma da sanya matakan kariya,” in ji Muhammed.
Bayan sayen kuri’u, jami’an INEC sun sake jaddada bukatar da suka dade suna yi na a kafa hukumar da ke yaki da laifukan zabe, suna masu cewa hukumar zabe ba ta da karfin gurfanar da masu laifi a gaban kotu.
A cewar Muhammed, “INEC na iya bakin kokarinta wajen ganin an gurfanar da masu laifukan zabe a gaban kotu, amma muna bukatar wata cibiya mai kwazo da ke da hurumin shari’a da kayan aiki domin gudanar da bincike tare da hukunta masu aikata laifukan zabe. Samar da hukumar zai tabbatar da cewa hukuncin sayen kuri’u, satar kuri’u, da sauran laifuffuka cikin gaggawa”.
Kwamishinan ‘yansanda mai kula da tsare-tsare da tantance harkokin zabe, Abayomi Shogunle, wanda ya wakilci babban sufetan ‘yansanda, ya yi nuni da cewa rashin isassun kayan aiki ya kan kawo cikas ga kokarin tabbatar da doka a lokacin zabe. “Muna fuskantar manyan kalubalen kayan aiki, tun daga tura jami’ai zuwa lunguna da sako da kuma tabbatar da sadarwa a lokacin zabe. Wadannan batutuwa ne da ya kamata a magance su idan ana son a aiwatar da dokokin zabe yadda ya kamata,” in ji Shogunle.
Da yake mayar da martani kan matsalolin da suka taso, shugaban kwamitin majalisar kan harkokin zabe, Hon. Adebayo Balogun, ya bayar da tabbacin cewa za a magance dukkan batutuwan da aka tattauna tare da sake fasalin zabe a nan gaba.
“Dokar zaben 2022, tana da matukar muhimmin wajen ci gaba, amma aiwatar da ita a babban zaben da ya gabata ya nuna wuraren da ke bukatar gyara. Mun himmatu wajen karfafa dokokin zabenmu don nuna gaskiyar dimokuradiyyarmu,” in ji Balogun.
Ya jaddada cewa, baya ga garambawul na majalisar, akwai bukatar kara wayar da kan jam’iyyun siyasa, jami’an INEC, da kungiyoyin fararen hula kan illolin da ke tattare da sayen kuri’u da sauran kura-kurai a zaɓen ƙasar nan.
কীওয়ার্ড: Zaɓe
এছাড়াও পড়ুন:
Hisbah ta rufe gidajen rawa a Katsina
Hukumar Hisbah ta rufe gidajen rawa da ke gudanar da harkokinsu a Jihar Katsina.
Hukumar ta umarci ɗaukacin masu gidajen rawa da ke gudanar da harkokinsu a cikin dare a faɗin jihar da su rufe.
Shugaban Hukumar, Dakta Aminu Usman ne ya bada umarnin tare da gargaɗin masu wuraren da matakin ya shafa.
Ya bayyana cewa ɗaukar matakin ya zama dole domin kare tarbiyya da dokokin addinin Islama da kuma barazanar tsaro a jihar.
Jami’an tsaron al’umma 6 sun mutu a artabu da ’yan bindiga a Sakkwato NAJERIYA A YAU: Tanadin Dokar Kasa Kan Kirkirar Gwamnatin Bibiya A KanoSanarwar da ya fitar ranar Laraba ta bayyana cewa tabbatar da tarbiyya da kare dokokin Musulunci sun zama wajibi.
Ya ci gaba da cewa, “za a ɗauki tsattsauran mataki kan duk masu kunne ƙashi, kuma ann riga an umarci jami’an tsaro da su tabbatar da bin wannan sabuwar doka.”