Ba ni da hannu a kisan Dele Giwa — Janar Babangida
Published: 21st, February 2025 GMT
Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta nesanta hannunsa da kisan gogaggen ɗan jarida kuma Babban Editan Jaridar Newawatch, Dele Giwa.
An kashe Dele Giwa wanda fitaccen mai sukar gwamnatin Babangida ne, ta hanyar wasikar bom a gidansa da ke Legas a ranar 19 ga watan Oktoban 1986.
Kwana biyu kafin kisan nasa wani babban jami’in Rundunar Leƙen Asiri ta Soji ya zargi Dele Giwa da yin fasa-kwaurin makamai da ƙasashen da nufin tayar da zaune tsaye a Najeriya
Sakamakon haka, dan jaridar ya yi hanzarin sanar da lauyansa, Gani Fawehinmi, game da halin da ake ciki.
Na yi nadamar soke zaɓen 1993 — Babangida NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi Ba —’Yan kasuwaAmma bayan kwanan biyu, wani babban hafsan soji, Kamar Halilu Akilu, ya kira waya ta ba Dele Giwa tabbacin cewa kuskure aka samu kuma an gano ainihin lamarin, don haka ya kwantar da hankalinsa, komai ya wuce.
Wani abokin Dele Giwa a Newawatch mai suna Ray Ekpu, ya ce bayan ’yan sa’o’i ne aka kai wani sako gwamnati gidan Dele Giwa.
Ray Ekpu ya bayyana cewa ɗan Dele Giwa mai suna Billy ne ya karbi sakon mai ɗauke da tambarin Fadar Shugaban Ƙasar ya mika wa mahaifin nasa, wanda a lokacin yake cin abinci tare da wakilin Newawatch na London, Kayode Soyinka, wand ya kawo mishi ziyara.
Wasikar mai ɗauke da tambarin Fadar Shugaban Ƙasa na kuma dauke da rubutun “wanda aka aika wa kaɗai zai buɗe.”
Amma a yanzu shekara 41 bayan kisan na Dele, Janar Babangida ya nesanta hannunsa ko masaniyar lamarin.
Babangida ya nesanta kansa da lamarin ne a littafin Tarihi da da ya ƙaddamar a ranar Alhamis a Abuja.
Babangida ya bayyana fatan cewa wata rana gaskiya ta yi halintama gano hakikanin musabbabin mutuwar Dele Giwa.
Ya bayyana takaici cewa ’yan jarida sun kawo koma baya ga binciken kisan, inda suka yi saurin yanke hukunci kafin a kammala binciken.
A cewarsa, ya yi fatan a lokacin da gwamantin farar hula ta Olusegun Obasanjo ta sake buɗe binciken kisan Dele Giwa ’yan sanda za su samo sabbin hujjoji da ke nuna abin da ya faru, amma hakan bai samu ba.উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dele Giwa kisan Dele Giwa
এছাড়াও পড়ুন:
An yi wa wata karya tiyatar ceton rai
Wata karya ta hadiyi safa 24 da sauran kayan sawa, inda suka makale masa a mukamuki – lamarin da ya haifar da yi masa tiyatar ceton rai a Jihar California a Amurka, kamar yadda cibiyar kula da dabbobi ta bayyana.
Wata karya mai suna Luna, jinsin Bernese Mountain da ta shafe wata 7 tana fama da rashin lafiya, sakamakon hadiye wasu kayayyaki na mamallakinta a ranar 16 ga Fabrairu bayan kamar yadda Cibiyar Ba da Agajin Dabbobi ta Corona ta ce a cikin wani sakon da ta wallafa a Instagaram.
Za a hukunta ma’auratan da suka ci zarafin yarinya a kan mangwaro — Zulum Majalisar Wakilai ta musanta karɓar kuɗi kan dokar ta-ɓaci a RibasLokacin da ta fara amai, an garzaya da ita zuwa asibitin dabbobi, inda wani likitan dabbobi ya bude cikinta, ya cire tufafin da ya haifar da toshewar hanjinta.
“Lokacin da ‘yan uwan masu karyar suka lura tana amai kuma tana cikin rashin lafiya mai tsauri, sai suka garzayo da ita wurinmu,” in ji cibiyar.
“Ba tare da bata lokaci ba, yanzu Luna yanzu ta fara kada wutsiyarta!” Ta kara da cewa “karyar tana da tsananin son safa “.
Cibiyar kula da lafiyar dabbobi ta saka hoton safa da aka cire daga hanjin karyar tare da hotunan D-ray na toshewar hanjinta, a cewar kafar Storyful, wanda ya fara gano labarin ceton karyar.
Wasu hotuna sun nuna Luna – tana wasa – cikin farin ciki da kwanciyar hankali a kan gadon asibiti, bayan an yi mata tiyata.
Cibiyar ta yi gargadin cewa, wadanda suka mallaki karnuka idan suka “lura suna amai, ko alamar rashin lafiya” sai su yi sauri su tuntubi likitan dabbobi.”
“Ita wannan karyar ta musamman ce, kuma muna farin cikin samun labarin murmurewarta,” in ji wani sakon da wani ya wallafa.