Trump Yana Son Ganin Bayan Shugaban Kasar Ukraine Volodimir Zelezky Daga Kujerar Shugabancin Kasarsa
Published: 21st, February 2025 GMT
A dai-dai lokacinda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana a fili kan cewa baya son nganin tokwaransa na kasar Ukraine Volodimir Zelesky kan kujerar shugabancin kasarsa. Al-amura suna kara tabarbarewa a Kiev.
Jaridar Economist ta kasar Burtaniya ta bayyana cewa al-amarin ya bayyana kiri-kiri ne a lokacinda shugaban kasar Amurka ya zanta ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimi Putin.
Jaridar ta nakalto wani babban jami’in gwamnati a Kiev yana cewa tun lokacinda suka fahinci cewa Trump baya son a ci gaba da yaki a Ukraine, sannan baya son shugaba Zeleski sun san haka zai faru.
Banda haka, Trump ya bayyana cewa Amurka ta kashe dalar Amurka miliyon 360 kan yakin da ta tabbatar da cewa Ukrain ba zata sami nasara ba. Banda wannan ya ji ta bakin Zeleski kansa kan cewa an sace rabin kudaden da Amurka ta bata. A halin yanzu dai Trump ya bukaci a gudanar da zabe a kasar Ukraine, don ya tabbatar da cewa Zelesky bai da magoya baya da yawa. A cikin watan Fabrairun da mukr ciki ne yaki tsakanin Ukraine da Rasha yake cika shekaru 3 da fara shi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rasha Ta Kakkabo Jiragen Sama Marasa Matuki 9 Na Kasar Ukiraniya
Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da cewa, ta kakkabo jiragen saman marasa matuki 9 da kasar Ukiraniya ta harba mata.
Sanawar ta ma’aikatar harkokin tsaron Rasha ta ci gaba da cewa; A daren jiya ne aka kakkabo jiragen sama marasa matuki 3 na kasar Ukiraniya da aka harba a kan yankin Biryansk, sai kuma wani jirgin saman guda daya akan sararin samaniyar Tatrastan. Bugu da kari makaman saman na Rasha sun kakkabo wasu jiragen sama marasa matuki guda 4 a sararin samaniyar “Bahrul-Aswad”, sai kuma jirgi guda daya a saman yankin Tula.
A gefe daya a jiya ne aka bude wani kwarya-kwaryar taro a tsakanin kasashen Amurka da Rasha a kasar Saudiyya domin tattauna hanyoyin kawo karshen yakin Ukinraniya.
Sakataren harkokin waje na kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa kasashen Amurka da Rasha sun kuduri anniyar kawo karshen yakin Ukrai.
A taron na jiya dai babu wakilin kasar Ukraine, wacce da alamun ta kasa samun nasara a yakin da ta shiga da Rasha kimani shekaru 3 da suka gabata.