MDD Ta CE Sake Tada Komatsar Tattalin Arzikin Kasar Siriya Zau Dauki Shekaru 50 Nan Gaba
Published: 21st, February 2025 GMT
MDD ta bada sanarwan cewa tattalin arzikin kasar Siriya na bukatar shekaru 50 nan gaba kafin ta koma kamar yadda take kafin yakin basasa a kasar.
Tashar talabijan ta Presstv ta nakalato shugaban hukumar UNDP Achim Steiner yana fadar haka a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa hukumar ta ta gudanar da bincike kuma ta gano cewa, rikici da yakin basasa da kuma mamayar kasar da sojojin kasashen yamma suka yiwa kasar, ya sa al-amura sun lalace a kasar, ta yadda idan tana bukatar komawa matsayinta kafin shekara ta 2011 tana bukatar rabin karni kafin hakan ya samu.
Tace Siriya tana bukatar zuba jari mai yawa a ko wace shekara kafin ta sami wannan ci gaban. A halin yanzu dai kasha 90% na mutanen kasar Siriya suna rayuwan talaka. Sannan kasha 50% daga cikinsu basa da aikin yi. Sannan tattalin arzikin kasar GDP na kasar yana rabin matsayinsa a shekara ta 2011. Banda tallafi daga kasashen waje kasar Siriya tana bukatar zuba jari mai yawa don komawa kamar yadda take.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Siriya tana bukatar
এছাড়াও পড়ুন:
Sarkin Qatar Ya Iso Tehran A Yau Laraba
Kamfanin dillancin labarun Qatar ( Qana) ya sanar da cewa, sarkin kasar Sheikh Tamim Bin Hamad ali-Sani ya baro Doha akan hanyarsa ta zuwa Tehran.
Majiyar ta kara da cewa, sarkin na Qatar zai zo da tawagar tattalin arziki da kuma siyasa. Baya ga batun tattalin arziki, bangarorin biyu za su tattauna batutuwan da su ka shafi Gaza da kuma Amurka, kamar yadda kamfanin dilllancin labaun Mehr ya nakalto.
Jakadan Jamhuriyar musulunci ta Iran a Qatar, ya saanr da cewa ziyarar da sarkin na Qatar zai kawo Tehran tana a karkashin kokarin bunkasa alakar kasarsa da Iran.