An tara Naira 16 a taron ƙaddamar da littafin IBB
Published: 21st, February 2025 GMT
Hamshakan attajirai da ’yan siyasa sun bayar da gudunmawar sama da Naira biliyan 16 a bikin kaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Taron ƙaddamar da littafin, mai suna ‘A Journey in Service’, wanda aka gudanar a Abuja ya tara manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya.
A nasa ɓangaren, Shugaban Rukunin Kamfanonin BUA, ya ba da gudunmawar Naira biliyan biyar.
Tsohon Ministan Taro kuma Shugaban Gidauniyar TY, Janar Theophelus Ɗanjuma, ya bayar da Naira biliyan uku.
Babban attajiri a yankin Kudu, Arthur Eze, ya ba da Naira miliyan 500.
Sanata Sani Musa ya ba da miliyan N250 a yayin da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ba da miliyan N50.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin ya ba da Naira miliyan 20 a yayin da Sanata Aliyu Wadada ya ba da miliyan 10.
Hamshakiyar ’yan kasuwa Folorunsho Alakija, da wasu fitattun ’yan Najeriya sun bayyana gudunmawa, amma ba su sanarna bainar jama’a ba.
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci tsoffin shugaban kasa na farar hula na mulkin soji irinsu Goodluck Jonathan, Yakubu Gowon, Abdulsalami Abubakar, da wasu manyan baƙi.
Tsoffin mataimakan shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da Muhammad Namadi Sambo da Yemi Osinbajo.
Hakazalika dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da takwaransa na Jam’iyyar LP, Peter Obi, sun samu halartar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Naira biliyan da gudunmawar
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Yi Tir Da Shugaban Hukumar IAEA Saboda Sanya Siyasa Da Daukan Bangare A Jawansa Na Baya Bayan Nan
Gwamnatin kasar Iran ta gargadi hukumar IAEA mai kula da al-amuran makamashin nukliya a duniya, bayan da babban sakataren kungiyar Rafaei Grossy ya fita daga matsayin dan ba ruwammu, a cikin harkokin siyasa a aikinsa, inda ya furta wasu jawabai dangane da shirin makamashin nukliya na kasar Iran.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Gorossi ya fita daga matsayinsa na gwararre da kuma masanin harkokin makamashin nukliya ya kuma dauki bangare a wani taro da yan jirudu da ya gabatar a birnin Tokyo na kasar Japan.
A cikin jawabin da yayi wa yan jaridu Grossi ya Iran tana ‘gasa makamashin Uranium har zuwa kasha 60% wanda ya kusan kaiwa ga makamashin Nukliya, sannan bata bawa hukumar IAEA hadin kai da yakamata.
Bayan wannan zancen na hukumar makamashin nukliya ta fitar da bayani inda take tuhumar Grossi da daukan bangare, kuma hukumarsa tana iya rasa iran ‘amincewar Iran’ da ayyukanta.