Iran Ta Yi Tir Da Shugaban Hukumar IAEA Saboda Sanya Siyasa Da Daukan Bangare A Jawansa Na Baya Bayan Nan
Published: 21st, February 2025 GMT
Gwamnatin kasar Iran ta gargadi hukumar IAEA mai kula da al-amuran makamashin nukliya a duniya, bayan da babban sakataren kungiyar Rafaei Grossy ya fita daga matsayin dan ba ruwammu, a cikin harkokin siyasa a aikinsa, inda ya furta wasu jawabai dangane da shirin makamashin nukliya na kasar Iran.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Gorossi ya fita daga matsayinsa na gwararre da kuma masanin harkokin makamashin nukliya ya kuma dauki bangare a wani taro da yan jirudu da ya gabatar a birnin Tokyo na kasar Japan.
A cikin jawabin da yayi wa yan jaridu Grossi ya Iran tana ‘gasa makamashin Uranium har zuwa kasha 60% wanda ya kusan kaiwa ga makamashin Nukliya, sannan bata bawa hukumar IAEA hadin kai da yakamata.
Bayan wannan zancen na hukumar makamashin nukliya ta fitar da bayani inda take tuhumar Grossi da daukan bangare, kuma hukumarsa tana iya rasa iran ‘amincewar Iran’ da ayyukanta.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: makamashin nukliya
এছাড়াও পড়ুন:
Brice Ologui Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Gaban Da Kashi 90.35% A Jiya Lahadi
Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Gabon wanda kuma ya jagoranci juyin mulkin da aka yiwa Ali Bongo tsahon shugaban kasar ya lashe zaben da aka gudanar a jiya Lahadi tsakanin yan takara 7 har da shi.
Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News” ya bayyana cewa Oligui dan shekara 50 a duniya, shi ne babban dogarin sojoji masu tsare fadar shugaban kasar Gaban, a lokacinda ya jagoranci juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin da yan gidan Bogo suka yi na shekaru kimani 50 a kasar.
Labarin ya kara da cewa kashi 2/3 na mutanen Gabon wadanda yawansu bai fi miliyon 2.3 ba suna cikin talauci a cikin kasa wacce take da arziki mai yawa.
Brice zai jagoranci kasar na tsawon shekaru 7 masu zuwa kuma yana iya sake shi takarar shugabancin kasa karo na biyu.
Yan takara 6 ne suka tsaya tare da Brice amma mai binsa bai sami fiye da kashi 3 % na kuri’un da aka kada ba sannan yawan fitowar mutane masu zabe ya kai kashi 70.4% wanda ya nuna cewa an sami sauyi babban a cikin harkokin siyasar kasar ta Gabaon.