HausaTv:
2025-03-24@11:42:23 GMT

Amurka Ta Bawa HKI Makami Mai Karfi, MK-87

Published: 21st, February 2025 GMT

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhafa barakammu da  sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masi muhimmanci a wannan makon wadanda suka hada da wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakewa tsaro na sauransu, da fatana masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yua.

//….. Madallah masu sauraro shirimmu na yau zia yi magana dangane da makamin bom masu suna MK-84 wanda kuma yake da Laba 2000 yake da katfin lalatawa da halaka mutane.

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyanan bayan ya dare kan kujerar shugabancin kasar Amurka ya aikawa HKI manya-manyan boma-bomai masu nauyin ton guda ko wannan ake kira MK-84. Kara kashe Falasdinawa, `wannan kuma a fila ya kara bayyana cewa  Amurka tana da hannun dumu-dumu a kissan Al-ummar Falasdinu a gaza.

Har’ila yau wannan ya nuna cewa HKI tana son ta maye gurbin makaman da ta rasa a yakin da ta gwabza fa Falasdnawa na kimani watanni 15 a Gaza, saboda a ranar lahadin da ta gabata ce sojoji HKI suka bada sanarwan cewa sun karmu makamai samfurin MK84-84 har guda 1,800 daga kasar Amurka wadanda shugaba Trump ya sanyawa hannu watan da ya gabata.

Sun isa tashar jiragen ruwa na Ashdod kuma tuni an kaisu sansanin jiragen saman yakin da ya dace.

Ministan yaki na HKI Isarel Katz ya godewa sabon shugaban kasar Amurka Donal Trump saboda goyon bayan da yake bawa HKI kan Falasdinawa. Musamman sabbon boma boman da ya basu wanda zai tabbatar da ikon HKI kan falasdinawa.

Ministan yakin ya kara da cewa tun bayan fara yaki a Gaza a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 HKI ta karbi taimakon makamai ton 76,000 mafi yawansu daga kasar Amurka. Ministan ya kara cewa wasu makaman sun shigo HKI ta jiragen sama 678 sannan sauran kuma ta jiragen ruwa 129.

Ya ce shugaba Biden ya aikawa HKI boma-boman MK84 a cikin watanni 7 na farko a yankin, amma cikin watan mayun shekarar da ta gabata ya dakatar.  Yayi haka ne don takurawar da kungiyoyi kare hakkin bil’adama a duniya. Wadanda suka damu da irin kissan kiyashin da HKI take yi a Gaza.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa Biden ya dakatar ne saboda zabubbuka masu zuwa a cikin watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, yana neman kuri’un Amurkawa wadanda suka damu da yadda HKI take nika Falasdinawa da wadannan boma-boman.

Sai dai duk da haka gwamnatin Biden bada dakatar da bawa HKI makamai da kuma tallafi ba duk tare da cewa bai sami nasara a zaben ba.

Bayan shigarsa white House shugaba Trump ya dage takunkuman bawa HKI makaman na MK87 a ranar 26 ga watan Jenerun shekara ta 20205.

Kasashen duniya da dama sun yi allawadai da shugaban Trump saboda dage wannan takunkumin, saboda akwai tsoron Natanyahu zai yi watsi da yarjeniyar tsagaita budewa Juna wuta a Gaza, ya ci gaba da kissan kiyashin da yakewa mutanen na Gaza.

Amma menen bom mai suna MK84 wanda ake magana a kansa. Masana suna cewa boma-bomai MK87 dai suna boma bomai mafi karfi wadanda gwamnatin kasar Amurka ta mallaka, kuma akwai wadanda ta fara kerasu tana kuma kara karfinsu kadan –kadan  har ya kai MK87.

Kafin haka dai Amurka ta fara kera makami ko boma bomai MK 80, sannan MK 81, sannan 82, sai 83.

Baoma-baman MK 87 dai sune mafi karfi daga cikinsu, wanda yake da karfinb fashewa da kuma lalata duk abinda aka jefashi a kai. Masana sun kara da  cewa nauyin Bom MK87 ya kai pound 2000 ko kuma kilogram 907.  An cikashi da sinadarin TNT da garin alumiium. Har’ila yau wani bangare na makaman na MK87, an yi shi da karfe, wanda kuma shi kasha 45% na dukkan nauyin makamin. Wannan kuma don samar da fashewa mai karfi idan ya fada kan wani abu.

Sannan ana amfani da jiragen yaki ne don jefa boma-boman MK87 kuma idan ya isa kan abinda ake nufi da shi sai yayi rami babban kafin ya fashi don tabbatar da cewa ya lalata wurin da aka jefa shi gaba daya. Idan ginie to ginin gaba daya zai fada kuma kuma rugurguje.

Masanan sun kara da cewa boma-boman MK87 suna iya huda konkere mai fadin cm 60-105, sannan zai tona kasa mai zurfin mita biyar kafin ya fashe. Idan kasar mai lauci ne kuma yana iya fin haka.

Sannan jiragen yakin da suke iya daukar irin wadannan boma boman sun hada da A-10, B-1B, B-52, F-4, F-15, F-16, F-111 da kuma F-117. Har’ila yau jiragen yakin kasashen Turkiyya da Saudiya da HKI suna da karfin daukar makaman na MK87.  Gwamnatin kasar Amurka ta fara amfani da irin wadannan makamai ne a shekaru 1970 a yakin Vetnam, sannan ta yi amfani da su a yakin Iraq, Yugoslavia da Afghanistan, hakama gwamnatin saudiya ta yi amfani da irin wadannan boma bomai a kan mutanen yemen. Sai kuma HKI ta yi amfani da irin wadannan boma bomai kan Falasdinawa a gaza da kuma mutanen kasar Lebanon a yakin tufanul Aksa.

Wadannan gwamnatoci dai suna amfani da wadannan boma bomai ne a mafi yawan lokuta kan gidajen mutanen inda za’a suke kashe mutanen fararen hula masu yawa.

HKI dai ta sha amfani da makaman MK84 kan falasdinawa ton shekara 1982 zuwa gaba, tare da amfani da jiragen yaki samfurin F16 da FF 15.

Banda haka HKI tana da makamai masu karfi fiye da MK87, kuma sun yi amfani da su kan falasdinawa ya fi a irga. Sun kama rusa gidajensu a kansu tare da amfani da irinsu.

Jiragen yakin HKI sun yi amfani da MK84 a kan cinkoson falasdinawa da kuma muatnen kasar Lebanon a garin Qana inda suka kashe yara 17 da manyan mutane 12 a birnin Beirut a shekara ta shekara ta 2006 a lokacin da ta fafata da kungiyar Hizbullah.

Sai dai duk tare da wadannan boma bimai ta kara samun nasara a kan kungioyar Hizbullah a yakin na kwanaki 33. Sai dai ta kashe fararen hula 1,400 tare da amfani da wadannan bomai boamai.

Sai dai duk tare da makaman da take da su, daga cikin har da MK87 wannan bai bata nasara a kan makiyanta ba.

Mun san cewa sojojin HKI sun yi amfani da makamai daban daban a yake yake daban daban da suka shiga da falasdinawa a Gaza ko kuma hizbullah a Lebanon amma basu sami nasara a dukkan yake –yaken ba.

Sannan ya yakinta na karshe na watanni 15 ma ta kasa cimma manufofinta a yakin gaba daya. Bata kwace gaza ba, bata bata kwace .

Haka kuma a yakin shekara ta 2023 ta kasa shiga kasar Lebanon.

Wani abin lura a yankin 7 ga watan octoba na shekara ta 2023, gwamnatin HKI ta kasa cimma manufofinta a Gaza da kuma kasar Lebanon, duk tare da barnan da suka yiwa shuwagabannin kungiyar Hizbullah da kuma Hamas.

Wannan yana tabbatar mana cewa yawan makamai da kuma sojoji ba sune suke bada nasara a yaki ba.

Sai dai sadaukawa, da nuna jarunta, har ‘ila da taimakon All..ga musulmi shi ne yake bada nasara kuma yake rusa makiya.

A shekara ta 2023 ko kuma a yakin 7 ga watan Octoba, har zuwa karshen yakin a ranar 19 ga watan Jenerun shekara ta 2025. Sojojin HKI sun rusa fiye da kasha 80% na zirin gaza. Amma kuma ta kasa samun kwato yahudawan da suke tsare a hannun Hamas, ta kuma kasa mamayar kasar Lebanon. Sojojin HKI basu taba rasa sojoji da fararen hula a yaki guda kamar yadda suka rasa a yankin Tufanul Aksa ba.

Sannan wani abin mamaki shi ne, makaman MK87 ba sabbon makami ne ga HKI ta taba amfani da sun a watanni 7 a farkon yakin tufanul Aksa, kamar yadda muka bayyana, kafin shugaban biden ya hanasu, don haka idan Trump ya mayar masu, wannan bay a nuna makaman zasu yi aiki fiye da yadda suka yi aiki a baya ba.

Masan suna ganin yakin Tufanul Aksa ya tabbatar da cewa HKI ba zata sake samun nasara a kan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ko kuma kungiyoyin Falasdinawa a Gaza ba, saboada sun yi amfani da dukkan makamai masu karfinda Amurka take da su amma sun kasa samun nasara a kan makiyanta. Don haka babu bambanci idan har sun yi amfani da makaman da suka kai karfin wadanda suka yi amfani da sub a ko wadanda suka fisu karfi.

Sannan wadannan kungiyoyi a gaza ko a kasar Leabanon sun sami makaman da zasu iya cillasu a kan yahudawa da cibiyoyin makamai na HKI a cikin haramtacciyar kasar, kuma ya tabbatar cewa garkuwan makaman da suka mallaka basa iya kakkabosu gaba daya, ya nuna cewa zaman lafiya ta kara a HKI Kenan.

Idan masu sauraro zasu tuna makamai masu linzami masu karfi wadanda suke kaiwa kan birnin Haifa da Tel Aviv ne suka tilastawa HKI neman tsagauita wuta da HKI a yankin na baya bayan nan.

Matukar wadannan makaman suna hannun kungiyar Hizbullah HKI ba zata kuskura ta farfa yaki da Hizbullah ba.

Shi yasa a halin yanzu tske son haka kai da wadanda suke tare da su a cikin gwamnatin kasar Lebanon ko kuma ma’aikatar leken asiransu don ganin sun raba hizbullah da makamanta , a sannan zasu sake famata da yaki idan har zuwa iya kwace makaman na kungiyar.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kungiyar Hizbullah da wadannan boma kan falasdinawa kan Falasdinawa shekara ta 2023 irin wadannan kasar Lebanon wadanda suka nasara a kan jiragen yaki kasar Amurka masu sauraro duk tare da

এছাড়াও পড়ুন:

Jagora: Amurka Ta Kwana Da Sanin Cewa Ba  Wata Riba Da Za Ta Ci Ta Hanyar Yi Wa  Iran Barazana

Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; Amurkawa su kwana da sanin cewa, babu wani abu da za su samu, ta hanyar yi wa Iran barazana, kuma waninsu ma ya sani cewa, idan har su ka aikata wani abu maras  kyau akan Iran, to za su fuskanci mayar da martani mai tsanani.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi a yau Juma’a dangane da bikin sabuwar shekara ta Noruz a Husainiyyar Imam Khumaini dake nan Tehran, ya bayyana cewa; Babban kusakuren ‘yan siyasar Amurka da kuma na  Turai , shi ne daukar ‘yan gwagwarmaya a wannan yankin da cewa  ‘yan koren Iran, da hakan batunci a gare su.”

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kara da cewa;  Al’ummar Yemen, kamar sauran ‘yan gwgawarmaya a cikin wannan yankin suna da dalilai na gwgawarmaya, Iran kuwa ba ta da bukatar ‘yan kore.”

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma kara da cewa; “Ko kadan, ba mu ne farau ba acikin wannan rikicin,amma idan wani ya fara aikata wani abu mummuna, to zai fuskanci  mayar da martani mai tsanani.

Jagoran juyin musuluncin ya kuma ce; Karshen abinda zai faru da gwgawarmaya shi ne cin kasar abokan gaba ‘yan  sahayonoya.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma ce; Abinda ‘yan sahayoniya marasa rahama suke yi,ya sosa zukatan al’ummu musulmi da wadanda ba musulmi ba.

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya yi bitar muhimman abubuwan da su ka faru a shekarar da ta gabata ta hijira shamshiyya da su ka hada mai daci da kuma dadi. Daga ciki ya bayyana hatsarin da faru a wurin hako ma’adanai na Tabas, dake arewacin Iran, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 50.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Firaministan Kasar Sin Ya Gana Da Sanata Steve Daines
  • Al-Huthi Ya Ce Kawo Wani Jirgin Ruwa Mai Daukar Jiragen Saman Yaki Gazawa Ce Ga Amurka
  • Iran Tace Zata Kaddamar Da Sabbin Magunguna Da Ta Samar Tare Da Amfani Da Makamashin Nukliya
  • Za’a Gudanar Taron Tattaunawa Tsakanin Rasha Ta Amurka A Karo Na Biyu 2 A Birnin Rayad na Kasar Saudiya
  • Jakadan Sin A Amurka: Mayar Da Karin Haraji Makami Kaikayi Ne Da Zai Koma Kan Mashekiya
  • An Aika Dan Canji Da Dan Walawala Gidan Yari A Kwara
  • Araghchi : Ya kamata Duniyar Musulmi ta dauki mataki mai karfi kan Isra’ila
  • Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da shirin noman rani na Lallashi
  • Saree: Filin jirgin saman Ben Gurion ba shi da aminci har sai an kawo karshen yakin Isra’ila a Gaza
  • Jagora: Amurka Ta Kwana Da Sanin Cewa Ba  Wata Riba Da Za Ta Ci Ta Hanyar Yi Wa  Iran Barazana