Babban mai kai wa Bello Turji makamai ya shiga hannu
Published: 21st, February 2025 GMT
Jami’an Tsaro a Jihar Sakkwato, sun kama babban mai yi wa Bello Turji safarar makamai, mai suna Hamza Suruddubu.
Rahotanni sun bayyana cewar ana zarginsa da yi wa wasu maharan safarar makamai a jihar.
An tara Naira 16 a taron ƙaddamar da littafin IBB Ba ni da hannu a kisan Dele Giwa — Janar BabangidaWata majiya, ta shaida wa Zagazola Makama cewa Suruddubu ɗan yankin Gabashin Sakkwato ne, kuma ya daɗe yana safarar makamai daga jihar Zamfara zuwa sansanonin ‘yan ta’adda a Gabashin Sakkwato.
“Shi ne babban mai yi wa ƙasurguman ’yan bindiga irin su Bello Turji, Boka, da Halilu Buzu safarar makamai,” in ji majiyar.
Bincike, ya nuna cewa ba makamai kawai Suruddubu ke safara ba, har da wasu kayayyakin buƙata kamar abinci da babura domin taimaka wa ’yan ta’adda a yankin.
“Har ila yau akwai rahotannin da ke nuna cewa wasu jami’an tsaro a ƙananan hukumomin Shinkafi da Isa na da hannu a safarar waɗannan makamai,” in ji majiyar.
Shugabannin al’umma da masana tsaro sun yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike a kan Suruddubu.
Sun buƙaci a yi binciken don gano yadda ake safarar makamai tsakanin Isa da Sabon Birni.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Safarar Makamai Zamfara zargi safarar makamai
এছাড়াও পড়ুন:
NDLEA Ta Kama Wani Mutum Mai Shekaru 75 Da Laifin Safarar Muggan Kwayoyi
A wannan rana a filin jirgin saman Legas, Babafemi ya ce jami’an ‘yansanda sun kama wata ‘yar asalin kasar Ghana mai shekaru 20, mai suna Parker Darren Hazekia Osei, mai shekaru 20 da haihuwa, dauke da fakiti 36 na Loud—wani nau’in tabar wiwi mai karfin gaske, a cikin wata katuwar jakar tafiya mai nauyin kilogiram 19.40.
Ya ce wanda ake zargin wanda ya bayyana kansa a matsayin dalibin Kimiyyar Kwamfuta a Jami’ar Gabashin Landan, ya taso ne daga birnin Bangkok na kasar Thailand ta hanyar jirgin Ethiopian Airlines, ya kuma amince ya dauko kayan a Bangkok domin kai wa Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp