Aminiya:
2025-04-14@18:12:37 GMT

’Yan sanda sun daƙile satar mutane, sun kama wasu 3 a Borno

Published: 21st, February 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta daƙile wani yunƙuri da ’yan bindiga suka yi na sace wani mutum a Sabon Garin Lassa da ke Ƙaramar Hukumar Askira Uba.

Rundunar ta kuma cafke wasu mutum uku tare da ƙwato wata bindiga ƙirar gida a hannunsu.

Babban mai kai wa Bello Turji makamai ya shiga hannu NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi Ba —’Yan kasuwa

Majiyoyin tsaro sun shaida wa Zagazola Makama cewa, lamarin ya faru ne a ranar 20 ga watan Fabrairu da misalin karfe 1 na dare.

Wasu ’yan bindiga huɗu suka kai hari gidan Mohammed Abubakar, mazaunin Sabon Gari Lassa, da nufin sace shi.

“Wanda suka yi niyyar sacewa ya yi ƙoƙarin kare kansa da adda, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa ba tare da sun cimma burinsu ba”, in ji majiyar.

Bayan haka, Abubakar, ya gaggauta kiran ’yan sanda, inda tare da haɗin gwiwar ’yan banga, jami’an tsaro suka bi sahun ’yan bindigar zuwa maɓoyarsu.

A sakamakon haka, rundunar ‘yan sanda ta cafke mutum uku da ake zargi, dukkaninsu mazauna ƙauyen Gajali da ke Ƙaramar Hukumar Askira Uba.

“Haka kuma an ƙwato wata bindiga da aka ƙera a gida daga hannun waɗanda ake zargin,” in ji majiyar.

Rundunar ’yan sandan jihar, ta yaba da yadda jami’an tsaro suka mayar da martani cikin gaggawa, tare da yin kira ga al’umma da su kasance masu lura da duk wani abu da ba su saba gani ba.

Ta kuma buƙaci su gaggauta kai rahoto ga jami’an tsaro domin ɗaukar mataki a kan lokaci.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Yan Sanda Askira Uba hari Satar Mutane

এছাড়াও পড়ুন:

Bam Ya Hallaka Mutane 8, Wasu da Dama Sun Jikkata A Borno

An ɗauki waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti a Maiduguri, inda ake ba su kulawar.

Har yanzu dai ba a tantance yawan waɗanda suka jikkata ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yansanda Sun Kama Wasu Da Ake Zargin Ɓarayin Wayar Wutar Lantarki Ne A Yobe
  • ’Yan bindiga sun kashe mutane 40 a sabon hari a Filato
  • ‘Yansanda Sun Gano Haramtaccen Wurin Hada Makamai A Kano
  • An kama kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano
  • An kama miyagun kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano
  • Bam Ya Halaka Mutum 8, Ya Jikkata Wasu Da Dama A Borno
  • Mutum ɗaya ya mutu a faɗan ƙungiyar asiri a Maiduguri
  • Bam Ya Hallaka Mutane 8, Wasu da Dama Sun Jikkata A Borno
  • Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro
  • Kashe-kashen Filato: Jami’an tsaro na sassauta wa masu laifi —Tsohon gwamnan soji