Malamai Na Karbar Horo Akan Shirin Ilimin Mata Na AGILE a Jigawa
Published: 21st, February 2025 GMT
Shirin karfafa karatun mat (AGILE), ya fara horar da Malamai 20 na kwanaki 3 domin gudanar da shirin ba da ilimi na zamani mai suna dama ta biyu ta samun ilimi. “Second chance education bangaren” a Kano.
Shugabar Bangaren Aikin, Miss Hafsat Adhama, ta bayyana haka a wajen taron cin abincin rana da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.
Ta bayyana cewa, sama da malamai 300 ne suka gabatar da aikace-aikacen kuma an tantance su bisa la’akari da cancantarsu, da gogewa a fannin ilimin boko, fahimtar yanayin gida, da kuma sha’awar yara mata masu tasowa.
Ta yi nuni da cewa, tsarin ya ƙare ne a zaɓin ƙwararrun malamai 60, tare da tabbatar da cewa an zaɓi mafi kyawun kayan aiki da ma’aikata ne kawai don tallafawa shirin AGILE.
Miss Hafsat Adhama ta ce, wannan tsattsauran tsarin zaɓen, yana ƙara jaddada himmar shirin AGILE da abokan haɗin gwiwarsa, na samarwa ‘yan mata ilimi dama na biyu mai ma’ana don samun kyakkyawar makoma.
Ta kuma bayyana cewa, kimanin cibiyoyin koyo 60 ne aikin ya gano a wurare daban-daban a fadin kananan hukumomi 44 na jihar Kano. Don haka Hafsat ta umurci wadanda suka ci gajiyar shirin da su mai da hankali a lokutan horon
A nasa jawabin, mai ba da shawara kan harkokin fasaha na shirin Farfesa Auwal Halilu ya jaddada muhimmancin wannan horon, inda ya ce horo ne na musamman da ke bukatar maida hankali.
Ya kuma bukaci mahalarta taron da su kula domin akwai gibi mai yawa tsakanin ilimin boko.
Farfesa Halilu ya bukace su da su kasance masu sada zumunci da saukin kai, domin sanya ilimin da ake bukata a cikin zukatan daliban.
A yayin gabatar da nasa jawabin, kodinetan aikin, Alhaji Mujittapha Aminu ya ce, tantance cibiyoyin koyo ya ba da fifiko wajen samun dama, aminci da taimakon al’umma.
A cewarsa, samar da ababen more rayuwa don samar da yanayi mai kyau da kwanciyar hankali ga ‘yan mata masu tasowa, su ma abubuwan da aka yi la’akari da su wajen zabar wuraren koyo.
Ya kara da cewa, an gano sama da cibiyoyin koyo 100 a fadin kananan hukumomi 44, amma duk da haka an kammala tantance cibiyoyin koyo guda 20.
Alhaji Mujttapha ya jaddada cewa, za su tabbatar da cewa an zabo ma’aikata masu inganci don tallafawa shirin AGILE.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, Shirin Koyar da ’Yan Matan Matasa (AGILE) da ke Kano, wani muhimmin shiri ne da aka tsara don samarwa ‘yan mata masu tasowa damar samun ingantaccen ilimi na biyu ta hanyar guraben karatu na yau da kullun.
Shirin yana da nufin cike gibin ilimi ga ‘yan matan da ba sa zuwa makaranta, inganta daidaiton jinsi da karfafawa ‘yan mata matasa ilimi da dabarun rayuwa masu mahimmanci don ci gaban kansu da zamantakewa.
USMAN MZ
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Sun Yi Fatan Al-Khairi Ga Iran Da Amurka A Tattaunawar Shirin Nukliyar Kasar
Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa na yankin tekun Farisa (PGCC) ya yi fatan alkhairi ga kasashen Iran da Amurka a tattaunawa ba kai tsaye ba a tsakaninsu dangane da shirin Nukliya ta kasar Iran na zaman lafiya wanda suka fara, a birnin Mascat na kasar Omman a ranar Asabar da ta gabata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jasem Mohamed AlBudaiw yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa, kungiyar tana bukatar gidan an warware matsaloli tsakanin kasashen duniya ta hanyar tattanawa. Haka ma tsakanin kasashen yankin.
AlBudaiw ya yabawa kasar Omman da shirya wannan tattaunawar, sannan ya yi fatan tattaunawan da aka fara zai kai ga rage tada jijiyoyin wuya a yankin da kuma kasashen duniya, ya kuma ce kasashen yankin suna fatan zasu kai ga sakamako mai kyau tsakanin kasashen biyu.
Gwamnatin kasar Iran dai tana har yanzun suna shakkar kasar Amurka saboda yawan yaudarar da tayiwa kasar a baya. Musamman fitar kasar daga yarjeniyar JCPOA a shekara ta 2018. Da kuma yawan takunkuman da ta dorawa a kasar tun lokacin.
Daga karshe babban sakataren kungiyar ta PGCC ya ce tana fatan za’a kawo karshen duk wani rikici a gabas ta tsakiya daga ciki har da na HKI a falasdinawa a Gaza ta hanyar tattaunawa da fahintar Juna.