Najeriya ta taɓarɓare bayan mulkin IBB – Obi
Published: 21st, February 2025 GMT
Dan takarar shugaban ƙasa a Jam’iyyar Leba (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce Najeriya ta daɗa taɓarɓarewa fiye da lokacin da tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja Ibrahim Badamasi Babangida ya bar mulki a shekarar 1992.
Obi ya bayyana haka ne a lokacin da yake tsokaci kan ƙaddamar da littafin tarihin Babangida da aka daɗe ana jira, mai suna ‘A Journey in Service’.
Aminiya ta gano cewa, ba a ba wa Obi damar shiga ba cikin zauren taron ƙaddamar da littafin ba, tare da wasu da dama da aka yi zauren taro na Congress Hall a otal din Transcorp Hotel, inda aka gudanar da taron saboda an kulle ƙofofin shiga bayan isowar Shugaba Bola Tinubu.
Obi, a saƙonsa da ya wallafa a shafin sada zumunta na X, ya bayyana cewa irin gudunmawar da IBB ke bayarwa ga tattalin arzikin Najeriya da gagarumin goyon bayansa ga harkokin kasuwanci da bunƙasar kamfanoni masu zaman kansu ba su da iyaka.
Da yake magana a kan abin da ya kira wasu muhimman abubuwa guda biyu na jawabin da IBB ya yi game da zaɓen 1993, ya ce Najeriya ba ta ci gaba ba kamar takwarorinta daga 1992 lokacin da IBB ya bar gwamnati.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Tsohon kocin Super Eagles Christian Chukwu ya rasu
Tsohon ɗan wasa, kuma tsohon mai horas da ’yan ƙwallon Super Eagles ta Najeriya, Christian Chukwu ya rasu.
Christian Chukwu ya rasu ranar Asabar yana da shekara 74.
Fashewar bam a mota ta kashe mutum takwas a Borno An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen FilatoChristian Chukwu ne kyaftin ɗin tawagar Super Eagles lokacin da Najeriya ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) ta 1980.
Dakta Olusegun Odegbami, tsohon ɗan wasan Najeriya kuma abokin Chukwu, ya tabbatar rasuwar mai ban tausayi a saƙon da ya wallafa ta manhajar sada zumunta X.
“Na samu labarin cewa tsakanin ƙarfe 9:00 zuwa 10:00 na safiyar yau Asabar, Christian Chukwu, MFR, wanda aka fi sani da Chairman abokina kuma abokin wasana, ɗaya daga cikin manyan ’yan wasan ƙwallon ƙafa a tarihin Najeriya, ya rasu.