Binciken Ra’ayoyi Na CGTN: Watan Daya Da Dawowar Trump Mulki, Mutanen Duniya Sun Ce Da Wuya A Ce An Gamsu Da Salonsa
Published: 21st, February 2025 GMT
Binciken Ra’ayoyi Na CGTN: Watan Daya Da Dawowar Trump Mulki, Mutanen Duniya Sun Ce Da Wuya A Ce An Gamsu Da Salonsa.
এছাড়াও পড়ুন:
Congo Da M23 Sun Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta
Gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da ƴan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda sun amince su dakatar da faɗa a gabashin ƙasar har sai an kammala tattaunawar sulhu da ke gudana a halin yanzu wanda Qatar ke shiga tsakani.
Wannan dai ita ce yarjejeniyar sulhu ta baya-bayan nan tun bayan da ƴan tawayen suka ƙara kai farmaki a gabashin ƙasar inda hukumomi suka ce an kashe mutane 7,000 tun daga watan Janairu.
A ranar Larabar da ta gabata ce, ɓangarorin biyu suka ba da sanarwar yin aiki tare don samar da zaman lafiya, bayan shafe sama da mako guda suna tattaunawa, wanda suka ce an gudanar cikin aminci tare da mutunta juna.
A watan da ya gabata, shugaban ƙasar Congo Félix Tshisekedi da takwaransa na Rwanda Paul Kagame suma sun jaddada aniyarsu ta tsagaita wuta ba tare da sharaɗi ba a wata ganawar ba-zata da suka yi a birnin Doha.
Rikicin da aka kwashe shekaru da dama ana gwabzawa ya ƙara kamari ne a watan Janairu, lokacin da ƙungiyar M23 ta ƙaddamar da wani farmaki da ba a taɓa ganin irinsa ba, inda ta ƙwace garuruwan Goma da Bukavu – manyan biranen ƙasar Congo guda biyu, lamarin da ya haifar da fargabar ɓarkewar yaƙi yankin baki ɗaya.
DR Congo na zargin Rwanda da bai wa ƙungiyar M23 makamai tare da tura dakaru domin tallafawa ƴan tawayen.
Duk da ikirarin da Majalisar Dinkin Duniya da Amurka suka yi, Rwanda ta musanta zargin da ake yi ma ta na goyon bayan ƙungiyar M23.