Hukumar bayar da gudunmawar fansho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta kulla yarjejeniyoyi da wasu mashahuran Hukumomin Asusun Fansho guda shida (PFA) da nufin tabbatar da tafiyar da kudaden fansho na jihar yadda ya kamata.

Shugaban ma’aikata na jiha Alhaji Muhammad K Dagaceri wanda ya jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin gwamnatin jihar Jigawa a gidan fensho na Dutse ya ce taron yana kara jaddada kudirin gwamnati na  tabbatar da gaskiya da inganci a tsarin tafiyar da fansho.

Ya kuma jaddada mahimmancin kula da harkokin kudi da kuma bukatar samar wa wadanda suka yi ritaya kudaden fansho domin ci gaba da gudanar da rayuwarsu.

“Wannan yarjejeniya ta nuna wani gagarumin ci gaba a kokarin da muke yi na ganin cewa ma’aikatanmu da suka yi ritaya sun samu haƙƙinsu a kan lokaci.”

Alhaji Muhammad Dagaceri ya ci gaba da bayyana cewa, an zabo shugabannin asusun fansho ne ta hanyar tantancewa.

A cewarsa, masu gudanar da ayyukan za su samar da ingantattun ayyukan gudanarwa, da suka hada da dabarun saka hannun jari, da kula da ayyukan asusu da inganta ayyukan abokan ciniki.

Shugaban Ma’aikatan ya ce Hukumar Fansho ta Jihar Jigawa za ta sa ido a kan hadakar, tare da tabbatar da cewa PFA sun bi ka’ida da kuma cika alkawuran da suka dauka ga Jihar da masu karbar fansho.

Ya jaddada sadaukarwar gwamnatin Gwamna Umar Namadi wajen kyautata jin dadin ma’aikatan da suka yi ritaya, yana mai cewa wannan wani bangare ne na kokarin inganta ayyukan gwamnati da kuma kaucewa rikon sakainar kashi a harkokin tafiyar da dukiyar jihar.

Da yake jawabi a madadin  hukumomin na PFA Manajan Daraktan Asusun Fansho na Premium Hamisu Bala Idris, ya tabbatar wa hukumar cewa PFA  da aka zaba za su ci gaba da aiki yadda ya kamata ta hanyar bin duk wasu sharuddan da ke cikin yarjejeniyar.

Hamisu, ya bayyana tsarin fansho na jihar Jigawa a matsayin wanda ya fi kowanne a fadin kasar nan.

A nasa jawabin, Shugaban  Hukumar  Fansho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomi, Dokta Bilyaminu Shitu Aminu ya bayyana cewa, zababbun  asusun fansho guda shida da za su kula da dukiyar hukumar su ne, Premium Pension Fund (Lead PFA), da PAL Pension, da GT Pension, da  NLPC Pension, da  Norrenberger Pension da Cruder.

Dakta Bilyaminu Shitu Aminu ya yabawa Gwamna Malam Umar  Namadi bisa gagarumin goyon bayan da ya bayar ga shirin da ya sa Jihar ta zama abin koyi a kasar nan.

Usman Muhammad Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa Yarjejeniya Jihar Jigawa jihar Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

UNICEF Ya Bukaci Hadin Kai Don Inganta Rayuwar Kananan Yara A Jigawa

Ofishin Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF da ke Kano, ya ce zai ci gaba da hada gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa a bangarori da dama da suka hada da kiwon lafiya, da ilimi, da samar da abinci mai gina jiki, da kare yara, da al’umma.

Shugaban ofishin , Mista Rahama Rihood Farah ya bayyana hakan a Dutse, babban birnin jiharJigawa.

Ya kara da cewa, hadin gwiwar da UNICEF ya yi da gwamnatin jihar Jigawa ya samu nasarori da dama, kamar karfafa tsarin tantance yaran da suke cikin kangin talauci, ta hanyar binciken da aka gudanar a kwanan baya (GHS), da samar da muhimman tsare-tsare da tsare-tsare, da kuma sanya masu ruwa da tsaki a tsarin.

Ya bukaci shugabannin kananan hukumomin da su bayar da gudunmawarsu wajen bada gudunmawarsu  domin magance halin kuncin rayuwa da kananan yara ke ciki a jihar Jigawa, ta hanyar amfani da kwararan hujjojin da za a yi amfani da su domin tsara bangarori daban-daban.

Ya ce binciken ya nuna cewa kashi 90 bisa 100 na yara a jihar Jigawa suna fama da matsanancin  kangin talauci, yayin da kimanin kashi 86 bisa 100 ke fuskantar rashi a fannoni masu muhimmanci da suka hada da kiwon lafiya, da ilimi, da abinci mai gina jiki, da tsaftataccen ruwan sha, da sauransu.

Mista Farah ya bayyana bukatar hada hannu cikin gaggawa domin rage radadin talauci da inganta rayuwar yara a jihar Jigawa.

“Don karfafa kokarinmu na hadin gwiwa, muna neman goyon bayan gwamnati wajen samar da matakan da za su tabbatar da yin amfani da bayanan da aka samu na kananan hukumomi domin gudanar da abin da ya dace”.

“Sauran fannonin sun hada da amincewa da ƙayyadaddun manufofin kare lafiyar jama’a, da amincewa da daftarin dokar kare al’umma da aka yi wa kwaskwarima zuwa doka, da ƙara yawan kason kasafin kuɗi don shirye-shirye na musamman na yara, da tabbatar da yin rajistar haihuwa ga yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar“, in ji Farah.

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilan ƙara kuɗin Jami’ar Gombe — Gwamna Inuwa
  • ‘Yan Fansho Na FRCN Da NTA Sun Yabawa Gwamnati Bisa Amincewa Da Biyan Harkokinsu
  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kaddamar Da Rangadi A Karamar Hukumar Jahun
  • UNICEF Ya Jinjinawa Jihar Jigawa
  • Shirin Rigakafin Cututtuka Na UNICEF/GAVI Ya Sami Cikakken Hadin Kan Gwamnatin Jihar Jigawa
  • Jihar Kano Ta Samar Da Wani Salo Na Bunkasa Ilmin Addinin Musulunci A Jihar
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Shirin Da’awah Na Mata A Jihar Jigawa
  • Matasan Jihar Jigawa Sun Karrama Gwamna Umar Namadi
  • UNICEF Ya Bukaci Hadin Kai Don Inganta Rayuwar Kananan Yara A Jigawa