MDD Ta Yi Gargadin Barkewar Yakin Da Zai Hada Kasashe A DRC
Published: 21st, February 2025 GMT
Manyan jami’an MDD dake aiki a nahiyar Afirka sun yi gargadi a yayin taron gaggawa na kwamitin tsaro akan cewa hare-haren da ‘yan tawaye masu samun goyon bayan Rwanda suke kai wa a gabashin DRC, zai iya haddasa yakin da zai hada kasashe da dama na yankin.
‘Yar sakon musamman ta MDD a DRC, Bintu Keita ta fadi cewa: “Ya zama wajibi ga kwamitin tsaron ya dauki matakan gaggawa domin hana barkewar yakin da zai hada kasashen yankin.
Shi kuwa dan sakon musamman na MDD a yankin tekun Victoria Huang Xia cewa ya yi; “Yadda mayakan kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 ta kwace manyan garuruwan da suke a gabashin kasar ta DRC a cikin makwannin bayan nan yana nuni da yadda ake fuskantar hatsarin taho mu gama a tsakanin kasashen yanki, fiye da kowane lokaci a baya.”
Jakadan kasar Faransa a MDD Nicolas De Riviere kira yi ga kwamitin tsaro da amince da daftarin kudurin da kasarta ta gabatar makwanni biyu da su ka gabata wanda yake jaddada wajabcin kare hadin kan kasar DRC da huruminta. Haka nan kuma ya yi kira da dakatar hare-haren M 23 da kuma janye sojojin Rwanda daga cikin kasar, sannan da bude tattaunawa.”
Jakadan ya kuma ce; Da akwai hatsarin barkewar yaki a cikin yakin, wanda yake karuwa a kowace rana.”
Kungiyar M 23 tana a matsayin gamayya ce ta kananan kungiyoyin ‘yan tawaye har 100 da suka shimfida iko a gabashin Congo dake da albarkatun karkashin kasa da tirliyoyin daloli.
Rwanda tana taimakawa ‘yan tawayen da sojojin da sun kai 4000 kamar yadda jami’an MDD da suke aiki a kasar su ka ambata. “Yan tawayen sun yi barazanar za su nausa su nufi babban birnin kasar Kinshasa mai nisan kilo mita 1,000.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন: