Limamin Juma’a Na Tehran Ya Jaddada Muhimmancin Hadin Kai A Tsakanin Al’ummar Musulmi
Published: 21st, February 2025 GMT
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a yau a birnin Tehran Hujjatul-Islam Wal Muslimin Muhammmad Hassan Abu Turabi Fard, ya ce; makiyan jamhuriyar musulunci ta Iran suna magana da sauti daya,yayin da juyin juya halin musulunci na Iran ya hada kasashen Lebanon,Yemen, Falasdinu,Iraki da wasu kasashen musulmi.
Limamin na Tehran ya kara da cewa, lokaci ya yi da al’ummar musulmi za su yi watsi da duk wani sabani a tsakaninsu, su dunkule su rika Magana da yawu daya.
Dangane da karatowar watan Ramadan mai alfarma, limamin na Tehran ya ce, watan Ramadan mai alfarma, wata ne na kara kulla alaka da Allah madaukakin sarki da karatun al’kur’ani.
Hujjatul Islam Wal Muslimin Abu Turabi ya kuma ce; Ma’abota alkur’ani mai girma su ne wadanda aka sani da yin rayuwa ta hankali da ilimi, kuma sakamakon wannan irin raywua shi ne samar da hadin kai da nesantar rabuwar kawuna.
Bugu da kari, limanin na Tehran ya ce hadin kai yana daga cikin sakamakon kare hakkin bil’adama, domin alkur’ani mai girma ya kiraye mu baki daya da mu kasance a tare da gaskiya da kuma tsarin musulunci.
Dangane da abinda Amurk ta mayar da hankali akansa a kiyayyarta da Iran, limamin ya ce shi ne yakin kwakwalwa da kuma farfaganda.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: na Tehran ya
এছাড়াও পড়ুন:
Fadar Mulkin Amurka: Tattaunawa Da Iran Ta Yi Armashi
Fadar mulkin Amurka ta “White Hosue” ta bayyana cewa tattaunawar da aka yi a tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci da wakilin Donald Trump akan gabas ta tsakiya Steve Witkoff, ta hanyar shiga tsakanin kasar Oman, ta yi armashi.
Da marecen jiya Steve Witkoff ya bayyana cewa; shugaba Donald Trump ya ba shi umarnin ya yi duk abinda zai iya domin rage tazarar sabanin da ake da ita ta hanyar tattaunawa da diflomasiyya.
Bayanin na fadar mulkin Amurka ya kuma yaba wa kasar Oman wacce ta kasance mai masaukin baki na tattaunawar da aka yi wacce ba ta gaba da gaba ba ce a tsakanin Amurkan da kuma Iran.
Gabanin bayanin na fadar mulkin Amurkan, manzon musamman na shugaba Donald Trump, Steve Witkoff ya fada wa tashar talabijin din NBC cewa, ya yi tattaunawa mai matukar armashi da kuma amfani.
Tun a ranar Asabar da safe ne dai ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci ya isa birnin Mascut, inda ya gana da takwaransa na kasar Sayyid Hamad Bin Hamud al-Busa’idi, tare da mika masa bayanai da su ka kunshi mahangar Iran akan tattaunawar.
Ministan na harkokin wajen Oman ya zama mai shiga tsakanin kasashen biyu a tsawon lokacin tattaunawar. Bangarorin biyu sun yi musayar takardu har sau hudu.
A ranar Asabar mai zuwa ne dai za a ci gaba da tattaunawar daga inda aka tsaya a wani wurin da ba a kai ga ayyana shi ba.