HausaTv:
2025-02-22@15:16:46 GMT

Thomas Friedman: Trump Yana Son Ci Gaba Da Zama Shugaban Kasar Amurka Har Abada

Published: 21st, February 2025 GMT

Fitaccen dan jarida na Amurka wanda  Patrick Heili ya yi hira da shi ta  Podcast, ya bayyana cewa; Shugaban kasar Amurka Donald Trump yana son ya ci gaba da zama akan kujerar mulki har abada.

Hirar da Thomas Friedman ta mayar da hankali ne akan salon mulkin Donald Trump da yadda yake son sauya yadda Amurka take a cikin kwanaki 100 na farkon mulkinsa.

Thomas Friedman ya ya bayyana yadda shugaba kasar ta Amurka Donald Trump yake kokarin kwaikwayon salon mulkin shugaban kasar China Xi Jin Ping da kuma na kasar Rasha Vladmir Putin da Fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.

Shi kuwa mai gabatar da shirin  Patrick Heili ya yi ta’aliki da cewa, Trump yana kallon wadannan shugabannin a matsayin masu karfi a cikin duniyar da take cike da raunana, kuma shi Donald Trump yana son ya shimfida ikonsa a cikin duniya baki daya.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ta Yi Tir Da Shugaban Hukumar IAEA Saboda Sanya Siyasa Da Daukan Bangare A Jawansa Na Baya Bayan Nan

Gwamnatin kasar Iran ta gargadi hukumar IAEA mai kula da al-amuran makamashin nukliya a duniya, bayan da babban sakataren kungiyar Rafaei Grossy ya fita daga matsayin dan ba ruwammu, a cikin harkokin siyasa a aikinsa, inda ya furta wasu jawabai dangane da shirin makamashin nukliya na kasar Iran.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Gorossi ya fita daga matsayinsa na gwararre da kuma masanin harkokin makamashin nukliya ya kuma dauki bangare a wani taro da yan jirudu da ya gabatar a birnin Tokyo na kasar Japan.

A cikin jawabin da yayi wa yan jaridu Grossi ya Iran tana ‘gasa makamashin Uranium har zuwa kasha 60% wanda ya kusan kaiwa ga makamashin Nukliya, sannan bata bawa hukumar IAEA hadin kai da yakamata.

Bayan wannan zancen na hukumar makamashin nukliya ta fitar da bayani inda take tuhumar Grossi da daukan bangare, kuma hukumarsa tana iya rasa iran ‘amincewar Iran’ da ayyukanta.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Yi Tir Da Shugaban Hukumar IAEA Saboda Sanya Siyasa Da Daukan Bangare A Jawansa Na Baya Bayan Nan
  • MDD Ta CE Sake Tada Komatsar Tattalin Arzikin Kasar Siriya Zau Dauki Shekaru 50 Nan Gaba
  • Tashar Jiragen Sama Ta Rafikul Hariri Int. Na Birnin Beirut Yana Ciki Da Masu Shiga Kasar Saboda Jana’izar Shaheed Nasarallah
  • Trump Yana Son Ganin Bayan Shugaban Kasar Ukraine Volodimir Zelezky Daga Kujerar Shugabancin Kasarsa
  • Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Cewa: Suke Da Hakkin Yanke Shawarar Makomar Kaarsu Ba Amurka Ba
  • Babban Kwamandan IRGC Ya Bayyana Cewa: Amurka Da Isra’ila Ba Su Yi Nasara A Yakin Gaza Ba
  • Palasdinawa Ne Zasu Fayyanace Makomarsu Ba Wasu Dan Mulkin Mallaka Ba: Qalibof
  • Trump Na Amurka Ya Zargi Shugaban Kasar Ukiraniya Da Kama –Karya Da Kuma Rusa Kasarsa Ba Tare Da Wani Dalili Ba
  • Wang Yi Ya Bayyana Ra’ayin Sin Kan Yadda Za A Karfafa Huldar Cude-Ni-In-Cude-Ka A Duniya