Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Taimakawa Shirye-shiryen Zabe A Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Saudiyya ta Gayyaci Kasashen Larabawa Kan Batun Kan Batun Gaza

Saudiyya ta kira shugabannin kasashen Larabawa na yankin Gulf da kuma Masar da Jordan a wani taron domin tattauna batun Gaza.

Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ne ya gayyaci shugabannin a taron na gobe Juma’a, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyyar SPA ya ruwaito.

Kasashen Larabawa sun yi alkawarin yin aiki a kan wani shiri na bayan yakin Gaza da kuma  sake gina Zirin a wani mataki na tunkarar shawarar shugaban Amurka Donald Trump na sake gina yankin da mayar da shi wurin shakatawa na gabar tekun kasa da kasa bayan korar mutanen Gaza zuwa wasu wurare.

Saudiyya ta ce taron na ranar Juma’a zai kasance ba na hukuma ba kuma za a yi shi ne cikin “tsarin dangantakar ‘yan’uwantaka da ke hada shugabannin,” in ji kamfanin SPA.

A cewar labarin, dangane da matakin da kasashen Larabawa suka dauka na hadin gwiwa da kuma shawarwarin da aka fitar dangane da shi, zai kasance cikin ajandar taron gaggawa na kasashen Larabawa da za a yi a Masar,” in ji SPA, yayin da yake magana kan shirin taron gaggawa na kasashen Larabawa da za a yi a ranar 4 ga watan Maris mai zuwa domin tattauna rikicin Isra’ila da Falasdinu.

Shi dai shugaban Amurka D.Trump ya yi kira ga kasashen Masar da Jordan su karbi Falasdinawa da ba su wajen zama bayan fitar da su daga Gaza, shawarar da kasashen suka yi fatali da ita.

Kasashen duniya da dama sun soki matakin na Trump, suna masu danganta shi da raba Falasdinawa da kasarsu ta gado.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • DRC : Kwamitin Tsaro Na MDD, Ya Yi Da Goyan Bayan Da Rwanda Ke Bai Wa ‘Yan Tawayen M23
  • Kasar Sin Ta Bukaci G20 Ta Zama Karfin Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali A Duniya
  •  Malaysia: An Bude Kiran Yanke Sayen Kere-kere Kamfanin “Tesla” Na Elon Musk
  • Jami’an Diblomasiyya Daga Kungiyar G20 Da Dama Sun Isa Afrika Ta Kudu
  • INEC Ta Buƙaci Majalisa Ta kirkiro Dokar Hana ‘Yan Siyasa Zuwa Rumfunan Zabe Da Maƙudan Kuɗaɗe
  • Saudiyya ta Gayyaci Kasashen Larabawa Kan Batun Kan Batun Gaza
  • Wang Yi Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Uganda
  • Dangote Ya Koma Matsayi Na 86 A Jadawalin Masu Arziƙin Duniya
  •  Jagora: Siyasar Kasar  Iran  Ta Ginu Ne Akan Kyautata Alaka Da Kasashen Makwabta