Leadership News Hausa:
2025-03-25@14:25:53 GMT

Kallon-Kallo: Ƙungiyar Ƙwadago Da ‘Yan Nijeriya

Published: 22nd, February 2025 GMT

Kallon-Kallo: Ƙungiyar Ƙwadago Da ‘Yan Nijeriya

Arangama Tsakanin NLC Da Gwamnatocin Soji

Ga duk mutumin da yai duba na tsanaki ga hakikanin manufofin samar da wannan kungiya ta NLC, la-budda, wajibi ne a rika samun sa-toka-sa-katsi tsakaninta da gwamnatoci musamman irin na Soja. Ba kawai gwamnatocin soja ba, da tafiya ta kara nikatawa kamar yadda za a gabatar nan gaba cikin wannan dan rubutu, an wayigari hatta gwamnatocin farar hula ma ba sa wanyewa lafiya da wannan madigar kungiya ta NLC.

A mabanbantan lokutan gwamnatocin Soji a wannan Kasa, an sha yin kwalli da kai farmaki tare da kame shugabannin wannan kungiya ta NLC, inda za a ga cewa, gwamnatocin, sun fi yin amfani ne da jami’an tsaro na farin kaya (DSS), wajen kai hare haren ga ‘yan kungiyar. Bugu da kari, fakam da yawa, jami’an tsaro kan tarwatsa tarukan ganawa da shugabannin kungiyar ke yi a tsakaninsu. Irin wannan kai sammaci ga’yan kungiyar, ya fi afkuwa ne a lokacin da masu bakin kaki (soja) ke jan ragamar Kasar.

Karkashin mulkin soja a Kasa, ta tabbata cewa, sau biyu ne gwamnatocin soja ke sanya kafa su ce sun ma rushe shugabancin kungiyar ta NLC na kasa kacokan. Ba don komai ba, sai don fito na fito ne da kungiyar ke yi game da wasu manufofin gwamnati da suke fassara su da ba alheri ba ne ba ga al’umar Najeriya, gabanin su fara warware alolarsu da tusa!!!.

Cikin Shekarar 1988 ne gwamnatin Soja karkashin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB, aka fara shelanta ruguje shugabancin kungiyar ta NLC. Ba don komai ba, sai don kin goyon bayansu ga wata manufar tattalin arziki da gwamnatin ta samar, wadda aka fi sani da SAP (Structural Adjustment Program). Jin haushin rashin samun goyon bayan NLCn ne ya jaza aiyana soke shugabancinta da gwamnatin IBB ta yi.

Cikin Shekarar 1994 ma, gwamnatin Soja karkashin Janar Sani Abacha, an soke shugabancin kungiyar ta NLC, ba don komai ba, sai don dagewa tare da kumajin kungiyar cewa, lallai ne Kasar ta Nijeriya da ta gaggauta komawa bisa turbar dimukradiyya, sai hakan ya zamto wani babban zunubin da zai wajabta yi wa jagorancin kungiyar rusau. Sannan, wata kitimurmura ta gwamnatocin Soja shi ne, a duk sa’adda suka rushe shugabancin kungiyar na kasa, sai kuma su nadawa kungiyar wani kantoma, don ci gaba da tafiyar da lamuran kungiyar, cikin salon da zai dace da soye-soyen zukatan masu damara, wato Soja.

Cikin Watan Janairun Shekarar 1999, bayan dawowar tsarin mulki irin na dimukradiyya a Kasar ne aka sami sukunin yin wasu gyare-gyare na musamman game da wasu dokoki da suke yin karen-tsaye ga kungiyar ta NLC a lokutan Soja. A wannan lokaci ne aka zabi tsohon gwamna Adams Oshiomhole a matsayin sabon shugaban kungiyar.

Ja-injar NLC Da Gwamnatocin Farar Hula

Tarihin Kungiyar ta NLC bai nuna cewa kawai tsakaninta da gwamnatocin Soja ne ba ta sami rashin fahimtar juna, sam, hatta tsakaninta da masu jagorantar mulkin dimukradiyya a Kasar sun kai ruwa rana! Lokaci ne da Kungiyar ke kan sharafinta da karsashinta, tare da samun kyakkyawar shaida daga akasarin jama’ar Kasa.

A farko farkon Shekarar 2000, an sami wata takaddama tsakanin kungiyar ta NLC da gwamnatin Obasanjo, ba don komai ba, sai don tashin farashin man fetur a Kasar. Wanda hakan ya faru ne sakamakon yunkurin gwamnati na rage adadi mai yawa na tallafi ga man fetur, tare da sallada yin farashin na mai a hannun ‘yan kasuwa’yan jari hujja. Nan take kungiyar ta NLC ta bazama daukar matakan yajin aiki a kai a kai cikin Kasa, a kan hanyarta na tilasa gwamnati yin mi’ara koma baya ga wannan sabuwar manufa tata na rage wani abu daga tallafin na fetur, tare da sallamawa masu manyan masu hada hadar man fetur din a Kasar, jan akalar sanya farashin feturin irin yadda suka so.

Cikin Watan Satumbar Shekarar 2004, kungiyar ta kwadago, ta bai wa gwamnatin Obasanjo wani wa’adin kididdigaggun kwanaki, na, ta canja matsayarta na sanya wani haraji a kan man fetur, ko kuma Kasar ta fuskanci wani gagarumin yajin aiki, duk da cewa wata babbar Kotun taraiya ta fadi cewa, kungiyar ta NLC ba ta da wani hurumi a doka da za ta yi shelar tafiya yajin aiki, kawai don wata manufa da gwamnati ta samar, duk da haka amma, kungiyar NLC, ta shelantawa jama’ar Kasa irin tsare-tsarenta game da tsunduma yajin aikin. A karshe dai jami’an tsaro na farin kaya ne aka yi zargin sun yi ciki da shugaban kungiyar na kasa Oshiomhole, wato sun kame shi.

Sai dai an hakkake cewa, mafi gawurtar zanga-zangar da kungiyar ta yi ita ce ta cikin Watan Janairun Shekarar 2012, a lokacin gwamnatin shugaba Jonathan. Yayinda ya tasamma bin shawarar babban kwamitinsa na tattalin arziki, inda suka hakkake cewa, Kasa na kan tafka asarar biliyoyin nairori game da sha’anin sanya tallafin man feturin. Sannan, aka ga cewa, bayan cire tallafin na mai, farashin litar mai ma zai tashi daga naira sittin da biyar (N 65) zuwa naira dari da arba’in da daya (N 141).

Wancan matsayi da gwamnatin Jonathan ke kokarin dauka, ya jaza kaurewar mummunar zanga-zanga a biranen Lagos da Kano da Fatakwal da sauransu. Wannan irin zanga-zanga da ba a taba gani ba, ta yi silar durkushewar duk wasu sha’anonin tattalin arzikin Kasa. Ala-tilas, sai da shugaba Jonathan ya baiyana yin wurgi da wannan manufa tasa a kafafen yada labarai sannan lamura suka kyautatu, game da wannan zanga-zanga da ake ta faman gabatarwa a cikin sakuna da lungunan Kasar.

Nan da nan mutum ba shi da ikon yankewa wannan kungiya ta NLC hukunci, ba tare da sanin irin nauyayen da ke bisa wuyayenta ba. Bugu da kari, Kungiyar, kan saka jama’ar kasa cikin wasu duffai a wasu lokuta, ta fuskanci kokarin dabbaka hukunci ga wata gwamnati, alhali sun shigar da irin wancan hukunci a mala, sa’adda suka fuskanci wata gwamnatin, alhali nau’in zunubinsu iri guda ne. Yayinda aka fara yin dalla dalla cikin lamuran Kungiyar a nan gaba, akwai yiwuwar mai karatu zai fi fahimtar inda aka sa gaba, ko a ce indagizo ke sakar!!!.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Kwadago shugabancin kungiyar gwamnatocin soja gwamnatocin Soja Kungiyar ta NLC kungiyar ta NLC kungiya ta NLC da gwamnatin da gwamnati

এছাড়াও পড়ুন:

Syria: SOHR ta fallasa jami’an tsaron sabuwar gwamnati na yi tsiraru kisan gilla

Kungiyar da ke sa ido da kare hakkin dan adam ta Syria (SOHR) ta fitar da fayafan bidiyo guda hudu da ke dauke da hotunan azabtarwa da kisa da jami’an tsaron sabuwar gwamnatin kasar  karkashin kungiyar Tahrir Sham  suke aiwatarwa a kan fararen hula tsiraru marasa rinjaye a kasar.

Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama a Syria ta bayyana a ranar Lahadi cewa, ta samu faifan bidiyo guda hudu ne da ke nuna yadda ake aiwatar da hukuncin kisa kan wasu matasa da ba sa dauke da makamai daga ‘yan Alawiyya, da jami’an tsaro suka aiwatar a kauyen al-Shir da ke yankin Latakia a ranar 7 ga watan Maris.

A cewar kungiyar, faifan bidiyon ya kara tabbatar da yadda aka aiwatar da kisan gillar da aka yi a yankunan gabar tekun Syria da kuma wadanda suka aikata hakan a kan fararen hula.

A cikin faifan bidiyo na farko ya nuna wasu matasa biyu sun durkusa a kasa yayin da jami’an tsaron sabuwar gwamnatin Syria  suke zaginsu tare da lakada musu matsanancin duka, duk kuwa da ikirarin da suka yi na cewa ba su aikata wani laifi ba.

A cikin wani faifan bidiyo na biyu, an nuna yadda aka azabtar da wasu fararen hula hudu  ciki har da tsofaffi biyu, da kuma tilasta wa daya daga cikinsu sumbaci takalmin wani jami’in tsaro.

Kaset na uku ya nuna irin mumunan duka da aka yi wa fararen hula da bindigogi da karafa kafin daga baya kuma duk aka kashe su.

Dukkanin wadanda suka aikata wadannan munannan laifuka dai sabbin jami’an tsaron sabuwar gwamnatin Syria ne da kungiyar Tahrir Sham mai dangantaka da kungiyar Alqaida ta kafa a Syria bayan hambarar da gwamnatin Bashar Assad.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Lebanon Ya Ce Basa Da Wani Shiri Na Samar Da Haldar Jakadanci Da HKI
  • Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Kafa Rundunar Daukin Gaggawa Don Magance Matsalolin Tsaro
  • An Ceto ‘Yan Nijeriya Sama Da 950 Daga Gidajen Yari A Libya – Gwamnati
  • An Ɗauko Sojoji Daga Waje Don Horas Da Dakarun Nijeriya 
  • An Ɗauko Sojoji Daga Wajen Don Horas Da Dakarun Nijeriya 
  • NUJ Ta Bada Tallafin Azumi Ga Iyalan Mambobinta Da Suka Rasu A Jihar Kebbi
  • Syria: SOHR ta fallasa jami’an tsaron sabuwar gwamnati na yi tsiraru kisan gilla
  • Al-Huthi Ya Ce Kawo Wani Jirgin Ruwa Mai Daukar Jiragen Saman Yaki Gazawa Ce Ga Amurka
  • Dole Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Ta Daina Barazana Ga Masu Sukar Ta – Amnesty
  • Dalilan Gwamnatin Tarayya Na Zuba Naira Tiriliyan 1.5 A Bankin Aikin Noma -Kyari